No menu items!

Sample Page Title

Date:

Faɗuwar ƙaramin jirgi ya hallaka mutane 2 a California

Wani ƙaramin jirgin sama ya rikito kan wani ginin kasuwanci a California a jiya Alhamis, inda ya hallaka akalla mutane 2 tare da jikkata wasu 18, a cewar ‘yan sanda.

Al’amarin ya faru ne da maraice a kusa da tashar jiragen saman birnin Fullerton, mai nisan kilomita 40 daga kudu maso gabashin Los Angeles. ba’a tantance musabbabin faduwar jirgin ba.

“An tabbatar da mutuwar mutane 2,” kamar yadda ‘yan sandan Fullerton suka wallafa a shafinsu na X.

KU KUMA KARANTA:Sojojin saman Najeriya, sun shirya bukin ƙarshen shekara a Katsina

Har ila yau, an kwantar da mutane 10 a asibiti sannan an yiwa wasu 8 magani a wurin da al’amarin ya faru.

Masu bincike basu tantance ko wadanda suka mutun fasinjojin ne ko kuma ma’aikata ne a ginin da jirgin saman ya fada, kamar yadda wani jami’in dan sanda ya shaidawa wata kafar yadan labaran KTLA da ke yankin.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...