Farfesa Jega ya caccaki Kotun Ɗaukaka Ƙara kan hukuncin zaɓen gwamnan Kano

0
140

Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya buƙaci a gudanar da bincike kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan rikicin zaɓen gwamnan Kano.

Alfijir labarai ta rawaito cewa kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja a ranar 17 ga Nuwamba, 2023 ta soke zaɓen gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da bayyana abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna na jam’iyyar adawa ta APC a matsayin wanda yayi nasara.

KU KUMA KARANTA: NNPP ta shigar da ƙara gaban Kotun Ƙoli kan shari’ar gwamnan Kano

Amma a cikin kundin bayanan hukuncin da kotun da aka fitar kwanaki huɗu bayan yanke hukuncin, ta bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen a ƙarshen takardar.

Jaridar ta rawaito cewa fitar takardar hukuncin ta haifar da ruɗani tare da gudanar da zanga-zangar adawa da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara a Kano.

Da yake magana a gidan Talabijin na Channels TV’s ta cikin shirin Politics Today, a ranar Litinin, Farfesa Jega ya bayyana hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na Kano da ke cin karo da juna a matsayin “abin takaici ne matuƙa.”

“Babu shakka… wannan sabon lamari da ya faru game da lamarin a Kano abin takaici ne. Baya ga Chidi Odinkalu, na ji kuma na karanta yadda manyan lauyoyi da yawa a Najeriya suna ƙalubalantar abinda ya faru.”

“Za ku yi tsammanin kotuna musamman a matakin ɗaukaka ƙara zasu yi irin wannan abun? Amma abin gaskiya abin mamaki ne.” Ina ji shi

A cewarsa “Yanayin da aka bayar a matsayin rubutaccen hukuncin ya saɓa wa wanda aka karanta a cikin kotun, tabbas hakan abin mamaki ne kuma abin takaici ne matuƙa.

“Na yarda, ni ba lauya ba ne, amma na yarda cewa akwai buƙatar a yi cikakken bincike akan wannan abu.” In ji Jega

Leave a Reply