Connect with us

Labarai

EFCC ta tsare masu sayar da sabbin takardun kuɗi a Kano

Published

on

Hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arzikin kasa ta tsare wasu ma’aikatan banki su shida kan zargin sayar da sabbin takardun kudi na Naira a Jihar Kano.

Jami’an hukumar EFCC sun kuma kama wasu ’yan kasuwa biya da ke harkar sayar da sabbin sabbin takardun kudin a jihar Kano.

Kakakin EFCC Dele Oyewale, ya ce an kama mutanen su 11 ne a ranar Litinin, bayan samun bayanan sirri kan harkallar da suke gudanarwa.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama manyan motoci 12 da mutum 41 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba

Jami’in ya bayyana cewa a yayin da ’yan kasuwar ke sayar wa jama’a sabbin takardun kudi, ma’aikatan banki kuma an kama su ne kan sayar da takardun kudin ga ’yan kasuwar da aka kama.

Hukumar ta ce za a gurfanar da dukkan mutanen 11 a gaban kotu nan ba da jimawa ba, idan aka kammala bincike.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

Labarai

Ɗangote ya soki sabon tsarin gwamnatin Tinubu

Published

on

Ɗangote ya soki sabon tsarin gwamnatin Tinubu

Ɗangote ya soki sabon tsarin gwamnatin Tinubu

Hamshaƙin Attajiri kuma Kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya yi kakkausar suka kan ƙarin kuɗin ruwa da babban Bankin Najeriya CBN ya yi wanda ya kai kusan kashi 30 cikin ɗari.

Da yake jawabi a ɗakin taro na Banquet dake birnin tarayya Abuja, yayin buɗe taron kwanaki uku da ƙungiyar masana’antun Najeriya (MAN) ta shirya, Ɗangote ya bayyana illolin da sabon tsarin kuɗin ruwan zai haifarwa wajen rage samar da ayyukan yi da kuma bunƙasar kamfanoni a ɓangaren masana’antu.

Ɗangote ya jaddada cewa idan aka samu kuɗin ruwa na kashi 30 cikin 100, ba zai yiwu a samar da ayyukan yi ko kuma bunƙasa masana’antu sosai ba.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta tashi a matatar man Ɗangote

Ya buƙaci gwamnati da ta aiwatar da sabbin tsare-tsare da zasu bayar da kariya da raya masana’antu na cikin gida, yana mai nuni da cewa manyan ƙasashen yammaci da gabashin duniya suna kare masana’antunsu sosai don tabbatar da ci gaba da yin takara ragowar kamfanonin ƙetare
“Babu wanda zai iya samar da ayyukan yi da kuɗin ruwa na kashi 30%. Babu wani ci gaba da zai samu,” in ji Ɗangote.

Ya kuma yi gargaɗi game da illolin dogaro da shigo da kayayyaki, inda ya kwatanta shi da shigo da talauci da fitar da ayyukan yi zuwa ƙasashen waje.
Kana ya jaddada mahimmancin samar da bashin kuɗaɗe masu rahusar kuɗin ruwa don samun ci gaba, sannan ya danganta rashin kariyar masana’antu da tabarbarewar tsaro, da ƴan fashi, da garkuwa da mutane, da talauci a ƙasar nan.

Continue Reading

'Yansanda

An tuɓe wa ’yan sanda 5 kaki kan karɓar cin hanci

Published

on

An tuɓe wa ’yan sanda 5 kaki kan karɓar cin hanci

An tuɓe wa ’yan sanda 5 kaki kan karɓar cin hanci

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tube wa wasu jami’an ta biyar kaki sakamakon zargin su da karɓar cin hancin kuɗi kimanin Naira miliyan uku.

Mataimakin Shugaban ’yan Sanda mai kula da Shiyya ta shida ta da ke Jihar Kuros Riba, Jonathan Towuru, ya sanar a Kalaba cewa ’yan sandan sun kwace kuɗin ne da bakin bindiga a hannun wani mai abin hawa.

A makon jiya ne aka zargi jami’an da ƙwayar kuɗin da bakin bindiga a hannun wani mutum da rundunar ta sakaya sunansa.

Yanzu haka waɗanda ake zargin an tuɓe masu kaki amma ana tsare da su ana bincike, da zarar an same su da laifi kotu za a turasu ta yanke masu hukuncin da ya dace.

KU KUMA KARANTA: ’Yan sanda za su tantance ’yan banga a Yobe

Mataimakin shugaban ’yan sandan ya ce waɗanda ake zargin su da karɓar cin hancin kuɗi Naira milyan uku daga wannun wani.

Ko a kwanan baya irin haka ta taba faruwa a kan babbar hanyar Kalaba zuwa Ikom inda aka kama wasu ’yan sanda kan karbar na goro.

Tafiya a kan hanyar na yawan zargin ’yan sanda da kula da shingen bincike a kan hanyar da yawan tatsar su kuɗi.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like