Hukumar Yaƙi da yi wa Tatalin Arziƙin Najeriya Ta’annati (EFCC) ta tsare tsohon gwamnan Babban Bankin ƙasar, Godwin Emefiele.
EFCC ta kama Emefiele ranar Alhamis da daddare, ƙasa da sa’a guda bayan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake shi.
Rahotonni na cewa EFCC na ci gaba da yi wa tsohon gwamnan na CBN tambayoyi, a shalkwatar hukumar da ke Abuja.
EFCC na tuhumar Emefiele kan zarge-zargen saɓa ƙa’idar aiki a lokacin da yake gwamnan CBN.
Cikin watan Yuni ne dai hukumar DSS ta kama Emefiele jim-kaɗan bayan shugaban ƙasar Bola Tinubu ya dakatar da shi daga aiki.