Connect with us

EFCC

EFCC ta mayar wa wata mata miliyan 19 da gida da mota

Published

on

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta miƙa kadarorin da ta ƙwato daga hannun wani ɗan damfara mai suna Aisosa Ohue, wanda aka fi sani da Frederick Leonard, ga wata Ba’amurke da aka kashe, Cheryldene Cook.

Kakakin hukumar Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

A cewarsa, kadarorin sun haɗa da zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 19 da kuma wani gida mai ɗaki uku da ke Ward 36A Amagba a ƙaramar hukumar Oredo ta Edo. Ya ce, kadarorin da suka haɗa da Lexus E350 saloon mota, iPhone 13 Pro Max da kuma wayar Samsung A31, kwamandan shiyyar, ACE I Adebayo Adeniyi da shugaban sashin zamba na 1 ne suka miƙa wa matar a Abuja, ACE II Jimoh Rauf.

Uwujaren ya ce Cheryldene Cook da ta taso daga ƙasar Amurka domin karɓar kayayyakin ta samu rakiyar lauyanta, Dakta Mike Nwosu a gaban hukumar.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama mutane 23 da ake zargi da damfara ta yanar gizo

Ya ƙara da cewa ta miƙa godiyar ta ga hukumar bisa samun sauƙi.

A cewarsa, Mai shari’a C.E Nwecheonwu na babban birnin tarayya, Kuje ya bayar da umarnin a ƙwace kadarorin a watan Janairu bayan da aka samu Orhue da tuhume-tuhume uku da suka haɗa da samun kuɗi ta hanyar ƙarya.

“Wanda aka yanke wa hukuncin ya yaudari wanda aka zalunta ne ta hanyar zamba ta soyayya yayin da yake nuna cewa shi shahararren ɗan wasan kwaikwayo ne, Frederick Leonard”.

2 Comments

2 Comments

  1. Pingback: Remi Tinubu ta ba da naira miliyan ɗari biyar ga ‘yan gudun hijira a Filato | Neptune Prime Hausa

  2. Pingback: Matuƙin Keke Napep ya mayar da miliyan 15 da wani fasinja ya manta a mashin ɗinsa | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

EFCC

Kotu ta ƙwace dala milyan 4 da dubu 700 da naira miliyan 830 da sauran kadarori daga hannun Emefiele

Published

on

Kotu ta ƙwace dala milyan 4 da dubu 700 da naira miliyan 830 da sauran kadarori daga hannun Emefiele

Mai Shari’a Yellim Ɓagoro ne ya ba da umarnin a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki, sakamakon buƙatar da lauyan Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa, Bilkisu Buhari, ta gabatar.

Babbar Kotun Tarayya dake Legas ta ba da umarnin wucin gadi na ƙwace fiye da dala miliyan 4 da dubu 700 da naira miliyan 830, da sauran kadarori da dama dake da alaƙa da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele.

Mai Shari’a Yellim Ɓagoro ne ya ba da umarnin a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki, sakamakon buƙatar da lauyan Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa, Bilkisu Buhari, ta gabatar.

KU KUMA KARANTA:CBN ya ba bankuna umarnin saka sabon harajin tura kuɗi

Bayan sauraron lauyan Hukumar EFCC, a hukuncin da ta zartar, Mai Shari’a Yellim Ɓagoro ta ce, “na saurari hujjojin lauyan masu ƙara sa’annan na nazarci buƙatar da aka gabatar tare da takardun dake mara mata baya.

An bayyana cewar kuɗaɗen da za a mayarwa gwamnatin tarayya a matakin wucin gadin na ajiye ne a bankunan “First da Titan da Zenith waɗanda Omoile Anita Joy da kamfanonin “Deep Blue Energy Services Limited da Exactquote Bureau de Change Ltd da Lipam Investment Services Limited da Tatler Services Ltd da Rosajul Global Resources Ltd da kuma Til Communication Nigeria Ltd ke gudanar da su.

EFCC ta doshi kotu ne domin neman ƙwace kuɗaɗen a matakin wucin gadi, ƙarƙashin sashe na 17 na dokar yaƙi da zambar kuɗaɗe ta 14 ta 2006, da sashe 44(2)(b) na kundin tsarin mulkin Najeriya kuma ƙarƙashin hurumin kotun.

Continue Reading

EFCC

EFCC za ta gurfanar da Hadi Sirika kan zargin N2.7bn

Published

on

Yau Alhamis za a gurfanar da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika a gaban kotu, kan badaƙalar naira biliyan 2.7.

Hukumar Yaki da Masu Karya Arzikin Kasa (EFCC) za ta gurfanar da Hadi Sirika tare da ’yarsa Fatimah da wasu biyu ne kan badakalar kwangilar Naira biliyan 2.7 da aka bankado a ma’aikatar sufurin jiragen sama karƙashin jagorancin Sirika.

An buƙaci Sirika da ya gurfana a gaban kotu tare Fatima da Jalal Hamma da kuma Kamfanin Al-Duraq Investment Ltd, a gaban Mai Shari’a Sylvanus Oriji na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama tsohon Ministan Jiragen Sama, Hadi Sirika

Ana tuhumar su ne da laifin yin amfani da mukamansu wajen karkatar da sama da Naira biliyan 2.7 daga ma’aikatar sufurin jiragan sama a zamanin shugabancin Hadi.

Karon farko ke nan da za a gurfanar da tsohon ministan a gaban kuliya.

Continue Reading

EFCC

Jerin sunayen tsofaffin gwamnonin da ake zargi da cin hanci ba daga wurinmu ya fito ba — EFCC

Published

on

Hukumar da ke Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Zagon-Ƙasa wato EFCC ta nesanta kanta daga wani jerin sunaye wanda ke yawo a wasu jaridu da kafafen sada zumunta da ke cewa tana bincikar wasu tsofaffin gwamnoni kan zargin rashawa.

A ranar Asabar ne wani labari ya rinƙa yawo kan cewa akwai tsofaffin gwamnoni 58 waɗanda hukumar ke bincika kan zargin almundahana ta kimanin naira tiriliyan 2.187 a cikin sama da shekara 25.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC Dele Oyewale ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana rahotannin a matsayin na ƙarya.

Mista Oyewale ya bayyana cewa waɗanda suka ƙirƙiri jerin sunayen su kaɗai suka san manufar da suke son cimmawa.

KU KUMA KARANTA: Idan ban kama Bello ba, zan yi murabus daga kujerata – Shugaban EFCC

“Hukumar EFCC, tana ganin ya zama wajibi ta nesanta kanta daga wani rahoto da ke yawo a kafafen watsa labarai na cewa ta fitar da cikakken jerin sunayen tsofaffin gwamnonin da ake bincike kan zargin cin hanci da rashawa.

“Rahoton mai taken: “EFCC ta saki cikakken jerin sunayen tsofaffin gwamnoni 58 da suka wawure tiriliyan N2.187”, a wata kafar watsa labarai, karya ne kuma hukumar ba ta fitar da wannan jerin sunayen ba ko kuma tattaunawa kan binciken tsoffin gwamnoni da wata kafar yada labarai,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sai dai a ƴan kwanakin da suka gabata hukumar ta EFCC ta yi ta bincikar wasu tsofaffin gwamnoni daga ciki har da tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello inda take zarginsa da cire dala miliyan 720 daga asusun jihar domin biyan kuɗin makarantar yaronsa.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like