EFCC Ta Kwato Wasu Kadarorin Da Sabon Mukaddashin Akanta-Janar Ya Mallaka Ta Hanyar Damfara

0
356

Daga; Rabo Haladu.

HUKUMAR yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), dake fafutukar kare sirrin tattalin arzikin kasa ta shiga binciken, sabon mai kula da ofishin Akanta-Janar na Tarayyar Najeriya (OAGF), Anamekwe Nwabuoku, a bisa zargin aikata manyan laifukan cin hanci da rashawa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa an nada Nwabuoku ne domin ya kula da ofishin akantan da aka dakatar, Ahmed Idris, wanda ya shafe sama da mako guda a hannun hukumar EFCC ana binciken sa kan badakalar naira biliyan 80.

Sai dai a cewar majiyoyin a ranar Litinin, mukaddashin AGF, ana tuhumarsa da cin hanci da rashawa da suka hada da karin albashin da ya yi wa kansa a hukumomin gwamnatin da ya yi aiki a baya.

Hakazalika hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun kwato wasu kadarorin da ya mallaka ta hanyar damfara.

Daya daga cikin majiyoyin ta sanar da Economic Confidental cewa daya daga cikin laifuffukan kudi na Nwabuoku da ake zargin an aikata shi ne a lokacin da yake daraktan kudi da asusu (DFA) a ma’aikatar tsaro.

Ana kuma zarginsa da aikata wasu ayyukan damfara da kuma amfani da tsarin gwamnatin tarayya (GIFMIS) wajen satar albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Leave a Reply