No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC), ta kama wasu tagwaye maza kan zargin damfara ta intanet, yahoo boys.

EFCC shiyyar Ibadan ta kama su ne a ƙauyen Apete kusa da Ibadan babban birnin Jihar Oyo, tare da wasu matasa biyar da ake zargin ’yan yahoo-yahoo ne.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta gurfanar da mata da miji a kotu kan zargin zambar naira miliyan 410

Hukumar ta ce rundunar ’yan sandan jihar ta miƙa mata wasu matasa uku da ’yan sandan suka kama bisa irin wannan zargi a lokacin da suke yin sintiri a Ibadan.

An sallami ɗaya daga cikinsu ba tare da beli ba, bayan an gano ba ya cikin tawagar tasu.

Kuma an gano wata ƙaramar mota ƙirar Toyota Corolla da iPhone guda 11 da sauran wayoyin salula.

Hukumar ta ce da zarar ta kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargin gaban kotu domin yanke masu hukunci.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...