EFCC ta kama shahararren mawaƙin Tiktok, da wasu 31 bisa laifin zamba ta yanar gizo

1
255

Jami’an hukumar shiyyar Kaduna na hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa, EFCC sun kama wani shahararren mawaƙi a Tiktok, Crown Uzama (aka ShalliPopi) da manajansa, Ajayi Abdul Hafeez (wanda aka fi sani da 21 Badda) bisa zargin zamba ta yanar gizo.

An kama su ne tare da wasu mutane 29 da suka haɗa da mata huɗu: Glory Chinyere Kelvin Ogunwa l, Tina Ochonogor, Favor Baba Dawa da Joseph Judith Iya.

Sauran sun haɗa da Adewale Adedokun, Yakubu Emmanuel Ojochememi, AbdulAzeez Temidayo Suleiman, Umoru Osioke AbdulAzeez l, Emmanuel Isaac Iwebo, Shuaibu Umaru Smart, Joel Kator, Gowon Titus, Emmanuel Daniel, Enough Etim Ekpo, Atano Timi Eben, Ijuo John Ochi, Paul Emmanuel Kaye, Uyit Victor da David Elijah Yachai. Sauran sun haɗa da, Leche Precious Sokomba, Onoja Samuel Uroko, Cornelius Oyathekhua Agbodesi, Edigim Nosa Success, Azubuike Melchizedek Oniya, Usman Shereef, Victory Dennis Chiemela, Lambert Fortunetus Chikwado, Asoore King Oloruntoba da Malik Adamu Jibril.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama mutane biyu da laifin daɓa wa matashi wuƙa, ya mutu har lahira

An kama su ne bayan samun bayanan sirri game da wani shiri da wasu da ake zargi da damfara ta Intanet suka shirya a Barnawa, Kaduna.

An kama waɗanda ake zargin ne a wani samame da suka kai a gidajen otal ɗin Disney Park Lounge, Epitome da Tomoso Hotels, duk a yankin Barnawa na Kaduna.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da wayoyin hannu da kwamfutocin tafi da gidanka da kuma motoci biyu.

Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu idan aka kammala bincike.

1 COMMENT

Leave a Reply