EFCC ta kama manyan motoci ɗauke da kayan abinci da za a fitar daga Najeriya

0
169

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa, EFCC, ta kama manyan motoci guda 21 maƙare da kayan abinci da za a fitar daga ƙasar.

EFCC ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata da daddare.

Ta ce jami’anta sun kama manyan motocin ne a kan hanyar Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama da ke jihar Borno.

“Ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2024, jami’an EFCC Shiyyar Maiduguri sun kama manyan motoci guda 21 maƙare da kayan abinci da kuma waɗanda ba na abinci ba a kan hanyarsu ta zuwa birnin N’djamena na ƙasar Chadi, da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Kamaru,” in ji sanarwar.

Hukumar ta EFCC ta ƙara da cewa bincikenta ya gano cewa “an yi dabara ne aka ɓoye kayan abincin a cikin manyan motocin ta yadda ba za a gane ba, amma zaratan jami’an EFCC masu-gani-har-hanji sun gano su.”

KU KUMA KARANTA: An ba da umarnin ƙara tsaro a rumbunan NEMA don gudun masu warwason kayan abinci

Ta ce an soma gudanar da bincike kan mutanen da kama a cikin manyan motocin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

“Ana sa rai kamen da aka yi wa motocin zai rage ƙarancin abincin da ake fama da shi a faɗin ƙasar sakamakon ayyukan masu fasa-ƙwauri,” a cewar EFCC.

Gwamnatin Nijeriya ta yi zargin cewa masu fasa-ƙwauri na da hannu a tashin farashin kayan abinci a ƙasar.

Ko a watan jiya sai da mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima ya ce an kama manyan motoci guda 45 ɗauke da kayan abinci da za a fitar daga ƙasar. Ya ƙara da cewa sun gano ɓarauniyar-hanya guda 32 da ake fitar da abinci daga Najeriya.

Leave a Reply