Rundunar shiyar Enugu na Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, (EFCC), a ranar Talata ta gurfanar da wani Manzo Uchechukwu Samuel a gaban mai shari’a H.O. Eya na babbar kotun jihar Enugu, jihar Enugu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar ta ce an gurfanar da manzo ne a gaban ƙuliya bisa tuhume-tuhume bakwai da suka haɗa da sata, haɗa baki da kuma samun kuɗi ta hanyar ƙarya.
Laifi ɗaya ya karanta, “cewa ku APOSTO UCHECHUKWU SAMUEL DA MR BISIRIYU ORIYOMI wani lokaci a shekarar 2019, a jihar Enugu dake ƙarƙashin ikon wannan Kotu mai girma, kun haɗa baki wajen aikata wani laifi; sata ta hanyar tuba kuma ka aikata laifin da ya saɓa wa sashe na 495 na dokar laifuka, Cap 30 Revised Edition (Laws of Enugu State of Nigeria), 2004.”
KU KUMA KARANTA: EFCC da Saudiyya sun cimma yarjejeniya don ƙwato kadarorin gwamnati da aka sace
Laifi na biyu, “cewa ku APOSTLE UCHECHUKWU SAMUEL AND MR BISIRIYU ORIYOMI tsakanin 21st August, 2019 and 17th December,2019 a Enugu, jihar Enugu dake ƙarƙashin ikon wannan kotun mai girma ta aikata wani laifi; yin sata ta hanyar zamba zuwa amfanin ka, jimillar Naira Dubu Biyar, Ɗari Huɗu da Talatin da Biyar (5,435,000.00), kasancewar ka mallakin Mista Eugene Onyegbulaonweya ne kuma ka aikata laifin sata saɓanin sashe na 342 da 343 na dokar Criminal Code Law, Cap 30, Revised Edition(Dokokin Jihar Enugu ta Najeriya) 2004 da hukuncin da ke ƙarƙashin sashe na 353(f) da (i) na doka daya”.
Ya amsa cewa “ba shi da laifi” lokacin da aka karanta masa duk tuhumar da ake masa.
Dangane da roƙonsa, lauyan masu shigar da ƙara Ani Ikechukwu Michael ya buƙaci kotun da ta sanya ranar da za a fara shari’ar.
Kotun ta bada belin wanda ake ƙara sannan ta ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 4 da 5 ga Yuli, 2023 don sauraren ƙarar.