DSS ta ce shugabanta bai sace kuɗin tallafi na ma’aikatan hukumar ba

0
192

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Najeriya DSS ta musanta zarge-zargen da ake yi kan cewa babban daraktan hukumar Magaji Yusuf Bichi ya yi sama da faɗi da kuɗin tallafi na ma’aikatan hukumar.

Mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya ne ya fitar da sanarwar inda ya musanta zargin da wani Jackson Ude ya yi a shafin X wanda ya yi zargin shugaban DSS din da kwashe kuɗin.

Afunanya ya tabbatar da cewa babu wasu kuɗi da aka bai wa hukumar a halin yanzu domin ma’aikata kuma da zarar an fitar da waɗannan kuɗaɗe za a bai wa ma’aikatan hakkinsu.

“Hukumar tana son sanar da cewa zarge-zargen da ake yi ba gaskiya bane. Hukumar na son tabbatar da cewa daraktan hukumar ko wani mai aiki da umarnin shi, babu a cikinsu wanda ya sace kuɗin tallafin da aka bai wa ma’aikata.

KU KUMA KARANTA: Sojoji da DSS sun daƙile yunkurin Boko Haram na kai hari a Kano

“Babu wani tallafi da aka bai wa hukumar kuma da zarar an bayar da shi, za a bai wa ma’aikatan hakkinsu,” in ji sanarwar.

Hukumar ta DSS ta buƙaci jama’a su yi watsi da ƙarerayin da ake yaɗawa waɗanda ke kawo rabuwar kai da kuma rikici.

Haka kuma hukumar ta tabbatar da cewa daraktan na DSS zai ɗauki matakai na shari’a dangane da lamarin.

Leave a Reply