Drogba, Obi Mikel sun shawarci Victor Osimhen ya tafi Chelsea

0
60
Drogba, Obi Mikel sun shawarci Victor Osimhen ya tafi Chelsea

Drogba, Obi Mikel sun shawarci Victor Osimhen ya tafi Chelsea

Ana ta dakon Chelsea ta ɗauko Victor Osimhen, ɗan wasan Najeriya da ke buga wasa a Napoli ta Italiya, yayin da ‘yan makonni ne suka rage a rufe kakar cinikin ‘yan wasa ta baraza.

Bayan da aka samu tabbacin cewa Osimhen na son barin Napoli ya ‘koma Chelsea’, tsaffin ‘yan wasan Chelsea, Didier Drogba da John Obi Mikel sun saka baki don jawo hankalinsa zuwa Stamford Bridge.

Tuni Napoli ta bayyana aniyar sayar da Victor Osimhen, sai dai zuwa yanzu ba a samu ƙungiyar da ta yi tayin da ya yi musu ba. A baya an samu raɗe-raɗin tayi daga PSG ta Faransa da ita kanta Chelsea a Ingila.

An yi ta samun tsaiko wajen tattaunawa tsakanin Chelsea da Napoli kan sayan Osimhen, inda batun yin musayarsa da Rumelu Lukaku yake ta jan ƙafa.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan wasan Man City bakwai sun tafi jinya

Sabon kocin Napoli, Antonio Conte, wanda kuma tsohon kocin Chelsea ne da ya yi aiki da Lukaku, ya bayyana aniyarsa ta son kawo Lukaku, wanda har yanzu yake da kwantiragi da Chelsea duk da ya je AS Roma a matsayin aro.

Zuwa yanzu dai Chelsea ta ɗauko tarin sabbin ‘yan wasa, ciki har da Pedro Neto, Kiernan Dewsbury-Hall, Marc Guiu, da Filip Jorgensen.

Sai dai ana sa ran za ta ɗauko haziƙin ɗan wasan gaba wanda yake da tarihin nasarori.

Waɗannan dalilai sun saka tsaffin zakarun na Chelsea, Didier Drogba ɗan asalin Ivory Coast, da kuma John Obi Mikel ɗan asalin Najeriya suke ƙoƙarin ganin Osimhen ya koma tsohuwar ƙungiyar tasu.

An ruwaito Mikel yana cewa, “Muna son wanda zai iya cika aiki, ya ciyo ƙwallo, da zura ƙwallo idan an ba shi. Wato gwani kamar Erling Haaland. Wannan shi ne abin da Victor Osimhen zai zo da shi Chelsea.”

“Ina fatan masoya Chelsea za su ga ranar zuwansa kulob ɗinmu. Zan tabbatar na tura masa saƙonni da kiran waya, don ganin cewa Chelsea ta zamo zaɓinsa! Amma dai alamu sun nuna yana son ƙungiyar kuma yana so ya zo Chelsea.”

A baya, wakilin Osimhen ya soki tunanin cewa ɗan wasan zai tafi Chelsea a matsayin aro.

A yanzu dai Osimhen na fatan ganin an kammala cinikin nasa cikin hanzari, saboda Napoli za ta fara buga wasanta a gasar Serie A na kakar bana ranar Lahadi tare da Verona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here