Donald Trump ya fara koro ‘yan Najeriya daga Amurka

0
150
Donald Trump ya fara koro 'yan Najeriya daga Amurka

Donald Trump ya fara koro ‘yan Najeriya daga Amurka

Daga Jameel Lawan Yakasai

Rukuni na farko na ‘yan Najeriya da gwamnatin Amurka ƙarƙashin Shugaba Donald Trump ta ware domin kora sun Kano hanya zuwa gida.

Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya tabbatar da hakan a wata hira da ’yan jarida, inda ya ce mutane 14 aka kora – ciki har da ’yan Najeriya da ɗan Gambia guda ɗaya.

Ya ce Ghana ta taimaka wajen mayar da ’yan Najeriyan ta hanyar mota zuwa ƙasarsu, yayin da ake ci gaba da shirya mayar da ɗan Gambian zuwa gida.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Trump na shirin ƙulla yarjejeniyar saka jari da Ukraine

Mahama ya bayyana cewa Amurka ta roƙi Ghana da wasu ƙasashen Afirka ta Yamma su karɓi bakin hauren da ake korawa, inda ya ce ƙasarsa ta amince saboda ’yan yankin ba sa buƙatar visa su shiga Ghana.

Sai dai ya bayyana dangantakar Ghana da Amurka a matsayin wadda ke cikin ƙalubale, musamman saboda karin haraji da takunkumin biza da Amurka ta ɗora kan ’yan ƙasarsa.

A ƙarƙashin gwamnatin Trump, Amurka ta kori bakin haure daga ƙasashe daban-daban ciki har da Jamaica, Vietnam, Laos, Eswatini, Sudan ta Kudu da Rwanda, duk da adawar da ƙasashe ciki har da Najeriya suka nuna.

Leave a Reply