Dole ne mutanen da suka wulaƙanta Al-ƙur’ani su fuskanci hukunci mai tsanani – Ayatollah Ali Khamenei

0
340

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jagoran addini na ƙasar Iran Ayatullah Ali Khamenei ya bayyana a yau Asabar cewa ya zama wajibi mutanen da suka wulaƙanta Al-ƙur’ani mai tsarki su fuskanci hukunci mai tsanani.

Ya kuma buƙaci ƙasar Sweden da ta miƙa waɗannan mutanen domin yi musu shari’a a ƙasashen musulmi, kamar yadda kafar yaɗa labaran Iran ta ruwaito.

“Dukkan malaman Musulunci sun yi ittifaƙi kan cewa waɗanda suka wulaƙanta Al-ƙur’ani sun cancanci hukunci mafi tsauri…Haƙƙin da ke kan wannan gwamnati Sweden shi ne miƙa masu laifi zuwa ga ƙasashen musulmi,” in ji Khamenei.

KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ta girgiza garuruwan Saudiyya, Iran, Masar da Lebanon saboda wulaƙanta Alkur’ani a Sweden

Malamai sun buƙaci a kashe wata yarinya da ake kyautata zaton ta zagi Annabi Muhammad (SAW).

Leave a Reply