Dangote ya yi ritaya a matsayin shugaban kamfanin sa

0
171
Dangote ya yi ritaya a matsayin shugaban kamfanin sa

Dangote ya yi ritaya a matsayin shugaban kamfanin sa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Aliko Dangote ya yi ritaya daga matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwa na kamfanin sukari mai suna Dangote Sugar Refinery PLC, wanda hakan ya kawo karshen jagorancinsa na tsawon shekaru 20 a kamfanin.

Ritayar tasa za ta fara aiki daga ranar 16 ga Yuni, 2025, bisa wata sanarwa da sakataren kamfanin, Temitope Hassan, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.

KU KUMA KARANTA: Kamfani na ne ke biyan haraji mafi yawa a Najeriya – Dangote

Dangote, wanda ya kasance shugaban kamfanin tun daga shekarar 2005, ana danganta masa gagarumar nasara wajen mayar da Dangote Sugar jagora a kasuwar masana’antar sukari a Najeriya, ta hanyar gudanar da manyan ayyukan fadada kamfani da kuma karfafa tsarin shugabanci mai nagarta.

Sanarwar ta bayyana cewa a lokacin shugabancinsa, kamfanin ya aiwatar da muhimman Ayyukan Haɓaka Noma a Jihohin Adamawa, Taraba da Nasarawa, don bunkasa samar da sukari a cikin gida da rage dogaro da shigo da kaya daga waje.

Sai dai an nada Arnold Ekpe, wanda ke matsayin Darakta Mai Zaman Kansa, a matsayin sabon shugaban kamfanin.

Leave a Reply