Dan Majalisar Tarayya ya maka ƴan mazabarsa a gaban Kotu a Kano

0
140
Dan Majalisar Tarayya ya maka ƴan mazabarsa a gaban Kotu a Kano

Dan Majalisar Tarayya ya maka ƴan mazabarsa a gaban Kotu a Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bagwai da Shanono Hon Yusuf Ahmad Badau ya maka yan kungiyar Bagwai/Shanono Together for Progress a gaban kotu biyo bayan da suka kai kararsa hukumar yaki da rashawa ta ICPC.

Inda suka shigar da korafin cewa a binciki dan majalisar nasu kan ayyukan mazabunsu.

KU KUMA KARANTA: Kotu a Kano ta tura Mutane 29 da ake zargi da Kashe DPOn Rano gidan Yari

Sai dai ko da Wakilin Jaridar Neptune Prime ya tuntubi lauyansa Barr. MM. Sani ya ce sun yi karar matasan ne a kan yin kungiya mara rajista da zargin batawa dan majalisa suna.

Ya ce, aikin dan majalisa nemo aiki ne, amma ba shi ne ya ke aiwatar da ayyukan ba.

Ya kara da cewa, akwai mamaki yadda matasan suka cakuda ayyuka da dama da ba su da alaka da dan majalisar.

Leave a Reply