Daliba ‘yar shekara 10 dake yin tafiyar kilomita 4 a kullum don zuwa makaranta

0
178
Daliba ‘yar shekara 10 dake yin tafiyar kilomita 4 a kullum don zuwa makaranta
Yarinyar ne tare da mai unguwa

Daliba ‘yar shekara 10 dake yin tafiyar kilomita 4 a kullum don zuwa makaranta

Daga Shafaatu Dauda Kano

A safiyar yau, 14 ga Yuli 2025, da misalin ƙarfe 7:00 na safe, an gano wata daliba mai ƙwazo wadda kullum sai ta shafe tsakanin kilomita 3 zuwa 4 tana tafiyar kasa kafin ta isa makarantar Firamare ta Irshadul Ibadi Sani Mashall da ke cikin Karamar Hukumar Kura a jihar Kano.

Daliba Sadiya Haruna, Mai shekaru Kasa da goma, tana da himma ta musamman, kuma ba wai kawai tana isa makaranta da wuri ba ne kawai, a,a har ma tana zuwa kafin a buɗe ƙofar makaranta, sannan ta yi ta jira da shauƙi don fara karatu.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NEDC ta ƙaddamar da Makarantar Mega ta zamani a Potiskum (Hotuna)

Mai unguwa kuma shugaban makarantar Firamarer Garun-Malam, Alhaji Sunusi Sikifa, a yayin da yake hanyarsa ta zuwa ta shi makarantar, ya rusketa a bakin ƙofar makaranta a dai-dai lokacin da take dakon a buɗe kofa.

Wannan al’amari ya burge shi matuka, domin a cewar sa:
“Irin wannan daliba nan ita ce gatan al’umma. Dole mu tallafa mata.”

Wannan rayuwar dalibar ta zame abin koyi ga sauran ɗalibai. Tana wakiltar jajircewa, sadaukarwa, da ƙaunar ilimi duk da nisan hanya da ƙalubale.

Ya yi kira da sauran dalibai su yi koyi da dabi’un daliba, Sadiya.

Leave a Reply