Da yawan ‘Yan Film sun talauce – Jarumi Tijjani Asase

0
133
Da yawan 'Yan Film sun talauce - Jarumi Tijjani Asase

Da yawan ‘Yan Film sun talauce – Jarumi Tijjani Asase

Daga Jameel Lawan Yakasai

Jarumin masana’antar fim ta Kannywood, Tijjani Abdullahi Asase, ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta janye matakin hana saka tallukan magungunan gargajiya a finafinan Kannywood.

Gwamnatin jihar, ta hannun hukumar tace finafinai da ɗab’i ta jihar ce ta samar da hana saka tallan magungunan gargajiya a finafinan Hausa da kuma bakin tituna, inda ta ce ana amfani da kalamai na batsa da ka iya gurɓata tarbiyya.

KU KUMA KARANTA:Dokace ta bawa hukumar tace fina-finai damar tace kowanne nau’in Bidiyo – Isma’ila Afakallah

A wani faifen bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an hango Asase na kira ga gwamnatin da janye matakin duba da illar sa ga masana’antar Kannywood da dumbin masu aiki a karkashin ta.

A cewar Asase, masana’antar Kannywood ta talauce, inda masu shirya fim da jaruman duk su na cikin halin babu, kuma ta hanyar Sanya tallukan ne suke samu su rage asarar abinda suka kashe.

Leave a Reply