Da laifin ta’addanci kotu ta ɗaure Nnamdu Kanu, ya ka sa kare kansa 

0
158
Da laifin ta'addanci kotu ta ɗaure Nnamdu Kamu, ya ka sa kare kansa 
Nnamdu Kanu

Da laifin ta’addanci kotu ta ɗaure Nnamdu Kanu, ya ka sa kare kansa

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa shugaban ƙungiyar kafa ƙasar Biyafra, wato Indigenous People of Biafra (IPOB) da ke tsare, Nnamdi Kanu, hukunci a kan tuhuma ta biyu cikin tuhume-tuhumen ta’addanci da ake masa, tana mai cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da shari’ar su ba tare da wata shakka ba.

Laifin, wanda yake ƙarƙashin Sashe na 16 na Dokar Hana Ta’addanci ta 2013, yana ɗauke da hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai idan aka samu wanda ake tuhuma da laifi.

A cikin hukuncin sa, Mai Shari’a James Omotosho ya bayyana cewa umarnin “a zauna a gida” wanda Kanu ya bayar a faɗin yankin Kudu-maso-gabas — tare da barazanar tashin hankali da kuma aiwatar da shi ta hanyar amfani da ƙarfi — ya zama aikin ta’addanci.

Kotu ta lura da cewa wanda ake tuhumar bai da wata dama ta doka da za ta ba shi ikon taƙaita zirga-zirgar jama’ar ƙasa, tana mai jaddada cewa Shugaban Nijeriya kaɗai, ƙarƙashin Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki, shi ne yake da ikon sanya takunkumin motsi ta hanyar amfani da ikon dokar ta-ɓaci.

KU KUMA KARANTA: A ranakun 19 da 20 ga watan Maris za’a ci gaba da sauraron shari’ar Nnamdi Kanu

“Mutanen Kudu-maso-gabas ba za a umurce su da zama a gida ba daga wani mutum da ba jami’in gwamnatin tarayya ba ko na kowace gwamnati jiha,” inji alƙalin.

Mai Shari’a Omotosho ya ambaci bayanan shaidar da PW4 ya bayar, wanda ya yi aiki a Jihar Imo, ya kuma shaida cewa umurnin tilasta zaman gida na kowace Litinin ya bar birane har da gonaki babu jama’a tsawon shekaru.

Shaidar ta kuma danganta kisan tsohon hadimin shugaban ƙasa, Ahmed Gulak, ga wasu ‘yan bindiga da ke aiwatar da umarnin, inda ta nuna cewa an harbe Gulak har lahira kusa da filin jirgin sama yayin da yake ƙoƙarin tafiya a ranar 30 ga Mayu, 2021.

Rahoton likita da aka gabatar a matsayin Shaida PWK ya tabbatar da cewa Gulak ya mutu ne sakamakon harbin bindiga da wasu ‘yan bindiga suka yi masa, waɗanda ake zaton dakarun ƙungiyar ta’addanci ta Eastern Security Network (ESN) ne, wanda kotu ta bayyana cewa suna aiki ƙarƙashin umarni da jagorancin Kanu a matsayin shugaban IPOB.

“Bayar da umurnin tilasta zaman gida ba tare da wani ikon kundin tsarin mulki ba, tare da barazana, aikin ta’addanci ne,” inji kotun.

“Kuma wanda ake tuhuma bai gabatar da wata hujja da za ta kawar da shari’ar masu gabatar da ƙara ba, don haka ana ɗaukar cewa ya amince da hujjojin da aka gabatar.”

Alƙalin ya kammala da cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da abubuwan da ke cikin tuhuma ta biyu, wadda ta zargi Kanu da iƙirarin kasancewa memba kuma shugaban IPOB, ƙungiyar da aka haramta, saɓanin Sashe na 16 na Dokar Hana Ta’addanci.

“Saboda haka, wanda ake tuhuma an yanke masa hukunci kan tuhuma ta biyu,” inji Mai Shari’a Omotosho.

Ana sa ran za a yanke hukunci nan gaba, tare da kotu tana mai cewa hukuncin da doka ta tanada a kan laifin shi ne ɗaurin rai-da-rai ko kisa.

A baya dai, kotu ta yanke wa Kanu hukunci a kan tuhuma ta farko da ake masa bayan ta tabbatar da cewa Kanu bai gabatar da wata kariya ba ko ya ba da wani bayani da zai ƙaryata hujjojin masu gabatar da ƙara.

Yayin da yake yanke hukunci, Mai Shari’a James Omotosho ya bayyana cewa shari’ar masu gabatar da ƙara ta kasance ba a ƙalubalance ta ba sakamakon ƙin da Kanu ya yi na gabatar da cikakkiyar kariya, tare da fitar da shi daga kotu a farkon ranar saboda yawan rashin ladabi da ya nuna.

“Wannan kotu, saboda haka, ta tabbatar cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhuma ta farko ba tare da wata shakka mai ma’ana ba,” inji alƙalin.

“Saboda haka, wanda ake tuhumar an yanke masa hukunci kan tuhuma ta farko.”

Tun da farko a safiyar yau, sai da Mai Shari’a James Omotosho ya bada umurnin cewa za a ci gaba da shari’a — gami da yanke hukunci – ba tare da kasancewar Nnamdi Kanu a cikin kotun ba, saboda “rashin ladabi” da shugaban IPOB ɗin ya ci gaba da nunawa a cikin kotu.

Daga nan jami’an tsaro suka raka Kanu suka fitar da shi daga kotun.

Leave a Reply