Daga Ibraheem El-Tafseer
Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ce aƙalla mutane 487 ne suka mutu sakamakon cutar mashaƙo da ta ɓarke a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC.
Ya ce “an fara samun wannan cuta ne tun a watan Disamban 2022, kimanin wata 10 kenan.
“An yi ta samun mace-mace a nan da can cikin waɗannan watanni, kuma shi ne ya kai adadin waɗanda suka mutu zuwa 487 cikin watanni. Sai dai an samu raguwar mace-mace a ‘yan kwanakin nan,” in ji Kwamishinan.
Mutanen da ake da su a yanzu a asibiti da ke kwance sanadin wannan cuta, ba su fi ɗari da goma ba, wani abu da ke nuni da raguwar cutar in ji shi.
Ƙungiyar ba da agaji ta likitocin ta MSF ta wallafa wata sanarwa a shafinta na intanet, inda ta ce a birnin Maiduguri na jihar Borno, sai da ta ƙara gadajen kwanciya ashirin a ƙaramin asibitin yara na Gwange 111, inda yara 110 ke samun kulawa daga ƙungiyar tun daga watan Janairun wannan shekarar.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta tabbatar da ɓullar cutar mashako a jihar
A jihar Bauchi kuwa MSF ta ce tana kula da yara 21.
A shekarar 2021 kaɗai yara miliyan 25 ne ba a yi wa rigakafin ba sam sam ko kuma ba a kai ga kammala musu ba a ƙasar.