Cutar mashaƙo ta kashe mutane 1,191 a cikin watanni 17 a Najeriya – NCDC

0
49
Cutar mashaƙo ta kashe mutane 1,191 a cikin watanni 17 a Najeriya - NCDC

Cutar mashaƙo ta kashe mutane 1,191 a cikin watanni 17 a Najeriya – NCDC

Daga Idris Umar, Zariya

Cibiyar daƙile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa (NCDC) ta ce aƙalla mutane 1,191 ne suka mutu sakamakon cutar Mashaƙo daga watan Mayu, 2023 zuwa yau a faɗin Najeriya.

Dr. Muzzammil Gadanya, Manajan Al’amura, na Cibiyar Kula da Cutar ta Mashako wacce ake ƙira Diphtheria na Ƙasa, ya bayyana haka a ranar Laraba a Kaduna yayin taron bita kan ɓarkewar cutar.

Ya ce ƙasar ta samu rahoton zargin kamuwa da cutar Mashako fiye da mutum 38,000, yayin da aka tabbatar da fiye da mutum 23,000 sun kamu.

KU KUMA KARANTA: Ɓarkewar cutar mashaƙo ta halaka mutane 40 a Kano

Gadanya ya ce babban abin da aka fi mayar da hankali a taron bita shi ne duba yadda ake tunkarar cutar yanzu a Najeriya da kuma karfafa kokarin haɗin kai domin daƙile yaduwar cutar gaba.

Sai dai ya ce an samu raguwar yawan kamuwa da cutar  a kasar nan baki ɗaya.

Gadanya ya ce ana da rigakafin cutar a tsarin rigakafi na yau da kullum, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da kokari don tabbatar da nasarar daƙile cutar.

Taron ya samu halartar masana daga cibiyoyin lafiya na ɓangarori masu dama.

Leave a Reply