Cutar mashaƙo ta ɓulla a wasu jihohin Najeriya, ta kashe yara da dama a Yobe

Daga Ibraheem El-Tafseer

Cutar Mashaƙo, wadda a turance ake kiranta da ‘Diphtheria’ ana zargin ita ce ta ɓulla a garin Potiskum dake jihar Yobe, inda yara da dama suke mutuwa sakamakon wannan cuta. Ita wannan cuta tana fara wa ne da zazzaɓi, bushewar maƙogwaro, kumbura wuya da kuma wahalar numfashi.

Kasantuwar yadda mutuwar yaran ya yawaita, wakilinmu ya ziyarci Asibitin Ƙwararru dake garin Potiskum (Yobe State Specialist Hospital, Potiskum), inda shugaban sashen masu kula da marasa lafiya (HOD Nursing) Alhaji Bukar Mai Anguwa, ya shaida wa wakilinmu cewa, “an ware wa yaran da ake zargin suna ɗauke da wannan cuta ɗaki na musamman domin ba su kulawa ta musamman.

Ana ci gaba da gwaje-gwaje domin tabbatar da ita wannan cuta. Bukar ya ba da shawara ga iyayen yara da zarar sun ga alamun wannan cuta, su kawo yaran Asibiti, domin a ba su agajin gaggawa. Mafi yawan yaran da suka rasu ma, ba a Asibiti suka rasu ba, a gida ne” inji shi.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta yi gargaɗi kan ɓarkewar ƙwayar cuta mai saurin kisa

Rahotanni sun nuna cewa, Asibitin suna fuskantar matsalar rashin wadatattun magungunan da za a dinga kula da yaran da suke ɗauke da cutar da shi. A binciken da wakilinmu ya yi da kuma zanta wa da wasu daga cikin iyayen yaran da suka rasa ‘ya’yansu, a unguwannin Tandari, Misau Road, sabuwar Sakateriya, Arikime, Ramin ƙasa, Boriya, Ugwanda da Texaco yara sama da 35 ne suka mutu a cikin sati ɗaya.

Akwai gidan da yara biyar ne suka mutu, akwai mai yara uku da masu bibbiyu. Kuma ana ci gaba da samun rashe-rashen har yanzu.

Sannan yanzu haka akwai yara 42, da suke kwance ana ba su kula wa ta musamman a Asibitin Ƙwararru na Potiskum.

Likitocin suna koka wa da yadda iyaye ba sa kawo ‘ya’yansu asibiti da wuri. Mafi yawan yaran da suka rasu ma a gida suka rasu, ba a kawo su Asibiti ba.


Comments

2 responses to “Cutar mashaƙo ta ɓulla a wasu jihohin Najeriya, ta kashe yara da dama a Yobe”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Cutar mashaƙo ta ɓulla a wasu jihohin Najeriya, ta kashe yara da dama a Yobe […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Cutar mashaƙo ta ɓulla a wasu jihohin Najeriya, ta kashe yara da dama a Yobe […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *