Cutar kwalara da zazzaɓin ‘dengue’ sun kashe sama da mutane 100 a Sudan

0
212

Cutar amai da gudawa da zazzabin dengue sun yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100 tun daga watan Agusta, a cewar Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Sudan ranar Asabar.

Ma’aikatar ta ce mutum 1,049 ne suka kamu da kwalara, 73 suka mutu a Khartoum, da jihar Al-Jazira da ke kudancin birnin da kuma jihar Gedaref da ke yammacinsa.

Khartoum ya kasance fagen daga tun watan Afrilu lokacin da yaƙi ya ɓarke tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.

Dubban mutane sun tsere daga birnin Khartoum zuwa yankunan da ke da sauƙin rikici a jihohin Gedaref da Al-Jazira, inda ake fama da ƙarancin ruwa mai tsafta.

Ma’aikatar lafiyar Sudan ta ƙara da cewa zazzaɓin dengue wanda sauro ke haddasawa ya ɓarke a jihohi tara inda ya kama mutum 3,316, cikinsu kuma 49 suka mutu.

KU KUMA KARANTA: Cutar mashaƙo ta kashe mutane 117, wasu 1,796 sun kamu da cutar a Yobe

A Jihar Gedaref, wadda ke kan iyakar ƙasar da Ethiopia, mutum 2,152 sun harbu da cutar inda mutum 33 suka mutu.

Tun kafin yaƙin da aka soma a watan Afrilu, harkokin kiwon lafiya a Sudan na fama da ɗimbim ƙalubale wajen shawo kan cutukan da kan ɓarke bayan sauƙar damuna galibi a watan Yuni.

Yanzu lamarin ya ƙara taɓarɓarewa ganin cewa an yi luguden wuta a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da dama, sannan likitoci da dama sun tsere daga ƙasar, kana babu isassun magunguna.

Ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta ce kashi 70 cikin ɗari na asibitoci a yankuna da yaƙi ya fi ƙamari sun daina aiki.

Leave a Reply