Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce za su yanke hulɗar jakadanci da Isra’ila kan yaƙin da take yi a Gaza.
Tuni da ma Petro yake caccakar Firaiministan Benjamin Netanyahu sannan ya yi kira ga Afirka ta Kudu ta saka shi a cikin ƙarar da ta kai Isra’ila a kotun duniya kan zarginta da kisan ƙare-dangi a Gaza.
KU KUMA KARANTA: Jami’ar Columbia ta yi barazanar korar masu zanga-zangar adawa da yaƙin Gaza
“A yanzu kuma a gabanku, gwamnatin canji da shugaban ƙasar jamhuriya suna sanar da cewa gobe za mu yanke hulɗar jakadanci da Isra’ila…saboda kasancewarta gwamnati da shugaban ƙasa masu kisan ƙare-dangi,” in ji Petro a yayin da yake jawabi ga dandazon jama’a a Bogota, don tunawa da Ranar Ma’aikata da kuma goyon bayan sauye-sauyen Petro kan walwala da tattalin arziki.