Cire tallafin man fetur ya jawo hauhawar farashin mai a Najeriya

4
973

Dogayen layukan mai sun dawo a gidajen sayar da mai a faɗin biranen Najeriya tun bayan da sabon shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man.

A jiya Litinin ne Tinubun ya sanar da cire tallafin a jawabinsa na farko bayan rantsuwar kama aiki inda ya ce kasafin ba ya cikin kasafin kuɗin da ya gada daga gwamnatin Buhari.

Wasu rahotanni na cewa a birane irin su Lagos da Abuja ana sayar da man a wasu wuraren a kan kusan naira 600 a kan lita ɗaya ƙari daga 185 a kan lita a yau Litinin. Kamar a birnin Damaturu 350 ne litar mai a wasu gidajen man. Sannan ga dogayen layuka, saboda wasu gidajen man sun ƙi buɗewa.

KU KUMA KARANTA: Sabon Gwamnan Kano Abba Gida-Gida, ya naɗa shugaban ma’aikata da sakataren gwamnati

Sai dai kuma kamfanin mai na ƙasar NNPC ya sanar cewa akwai wadataccen mai a ƙasar saboda haka babu dalilin da zai sa mutane su shiga fargabar sayen man.

‘Yan ƙasar da dama na kokawa kan yadda suke shafe tsawon lokaci a kan layi domin sayen man.

Tinubu ya ce za a yi amfani da kuɗin tallafi wanda ya ce a yanzu wasu attajirai ne kawai suke cin moriyarsa, wajen bunƙasa wasu fannonin da jama’a za su fi amfana.

Ba a san ko tun daga jawabin nasa gwamnati ta dakatar da tallafin ba kenan.

Masana harkokin tattalin arziƙi na nuna cewa tasirin cire tallafin zai haddasa tsadar sufuri da kayayyaki.

4 COMMENTS

Leave a Reply