Cire tallafin mai: COEASU ta umarci malamansu da su yi aikin kwanaki biyu a mako

1
230

Ƙungiyar malaman kwalejojin ilimi, (COEASU), ta umurci membobinta a faɗin ƙasar nan da su riƙa zuwa aiki kwana biyu a mako har sai gwamnatin tarayya ta biya buƙatar ta na ƙarin albashin kashi 200 cikin 100.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban COEASU na ƙasa, Dakta Smart Olugbeko a Abuja ranar Laraba.

Mista Olugbeko ya ce an cimma wannan matsayar ne a wani taron ban mamaki da ƙungiyar ta gudanar a ranar Talata, a daidai lokacin da membobin ƙungiyar ke fuskantar wahalar samun aiki sakamakon ƙarin farashin man fetur.

KU KUMA KARANTA: Tinubu na neman majalisa ta amince da kuɗin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur

A cewarsa, aiwatar da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi watanni biyu da suka gabata ya ƙara farashin litar man fetur da kashi 250 cikin ɗari.

“Hakan ya ƙara ta’azzara hauhawar farashin kayayyaki da kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi tare da talauta al’ummar Najeriya.

“Ma’aikata, ciki har da ma’aikatan kwalejoji na ilimi, sun ci gaba da yin imani da gwamnati kuma sun zaɓi jure wahalhalun da ba za a iya mantawa da su ba suna tunanin zai kasance na ɗan lokaci kaɗan kamar yadda gwamnati ta yi alƙawarin fitar da matakan kwantar da hankali.

“Kaito! yayin da ƙarfinmu na ɗorewar fata ya riga ya ƙare, farashin man fetur ya ƙara tashi zuwa Naira 650 kowace lita.

“Yanzu haka shugabannin ƙungiyar sun mamaye ƙorafe-ƙorafen da membobin ƙungiyar ke yi na cewa ba za su iya zuwa aiki ba sakamakon ƙarin farashin man fetur da kuma tsadar sufuri,” inji shi.

Mista Olugbeko ya bayyana cewa ya zama babu makawa ƙungiyar ta umurci membobin su je aiki kwanaki biyu kacal a mako.

Ya ƙara da cewa za a ƙira taron gaggawa na NEC domin amincewa da matakin yanke takamaiman ranakun makon da membobin za su tafi bakin aiki.

“An amince da albashin ma’aikatan kwalejojin ilimi a 2010, shekaru 13 da suka gabata.

“Wannan yana nufin muna albashi ɗaya ne tun 2010 yayin da farashin man fetur ya tashi daga Naira 65 zuwa Naira 70 a 2010 zuwa N aira 650 a 2023 (ya ƙaru sau goma).

“Tsarin albashin mu wanda za a sake tattaunawa a tsakanin shekaru uku ya kasance a tsaye har tsawon shekaru 13, tare da tsallake tattaunawa guda huɗu.

“Muna ƙira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta yin abin da ake buƙata domin matakin da babu makawa ƙungiyar ta ɗauka kan wannan ƙuncin zai yi illa ga ɗaliban.

“Kamar yadda zai kai ga tsawaita kalandar ilimi – zangon karatun makonni 16 zai zama makonni 32 ko fiye; yayin da aikin koyarwa na watanni shida zai zama watanni 12,” in ji shi.

Shugaban na ƙasa, ya yi ƙira ga shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta magance matsalar daidaita albashin ma’aikatan kwalejojin ilimi.

1 COMMENT

Leave a Reply