Cin ‘Fara’ ya fi amfani a jikin ɗan’adam fiye da naman Kaji da na dabbobi – Likitoci
A wani rahoto da DW Hausa ta ruwaito, ta bayyana cewa binciken likitoci ya tabbatar da cewa “Cin Fara ya fi amfani a jikin ɗan’adam fiye da naman Kaji da na dabbobi ”
To su dai likitoci sun kafa hujja ne da yawan sinadarai masu amfani da gina jiki da ke jikin fara saboda itatuwan da take ci.
KU KUMA KARANTA: Yawan cin Kaza na haifar da kansar hanji – Bincike
To yanzu za a zura ido a ga ko wannan bincike na likitoci ko zai samu karɓuwa, ta hanyar hauhawar farashin Fara ɗin.









