Category: Fyaɗe
-
Fyaɗe: An ba da belin Dani Alves, tsohon ɗan wasan Brazil kan dala miliyan 1.1
Wata kotu a Sifaniya ta ba da belin tsohon ɗan ƙwallon ƙafar Brazil da kuma Barcelona, Dani Alves, kan dala miliyan 1.1. Sauran sharuɗɗan belin sun haɗa da cewa Alves zai ajiye fasfo ɗinsa na Brazili da na Sifaniya, domin gudun ka da ya fice daga Sifaniyar. A ranar Laraba ne wata kotun Barcelona ta…
-
Wani hedimasta ya yi wa ‘yar shekara shida fyaɗe
An kama wani hedimasta a jihar Bauchi da laifin yi wa ‘yar shekara 6 fyaɗe. Mai shari’a Nana Fatimah Jibrin, shugabar babbar kotun jihar Bauchi mai lamba 11, ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 11 a gidan kaso ga wani Hedimasta a garin Burra da ke ƙaramar hukumar Ningi mai suna Jalaludeen Zakari bisa samunsa da laifin yin lalata…
-
Kotu a Kebbi ta ɗaure yaron da ya yi wa ƙananan yara biyu fyaɗe
Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Birnin kebbi ta samu wani matashi ɗan shekara 16 Habibu Umar da laifin yin lalata da yara ƴan mata kuma aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan gyaran hali. Ɗan sanda mai gabatar da ƙara Insp. Muntari Mati, a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023, a…
-
An kama yaro ɗan shekara 16 a Kebbi bayan ya yi wa ƙananan yara 2 fyaɗe
An kama wani matashi ɗan shekara 16 Habibu Umar bisa zargin yi wa ƙananan yara biyu fyaɗe a unguwar Badariya a Birnin kebbi. An kama shi ne da sanyin safiyar ranar Talata 21 ga watan Nuwamba, 2023 bayan da ya ruɗe ƙananan yara mata biyu da ke zaune a Badariya zuwa wani daji da ke kusa tsakanin yankin Badariya da…
-
Tsoho mai shekara 70 ya yi wa yarinya kurma yar shekara 15 fyaɗe har ta mutu
Wata Kotun Majistare da ke zamanta a jihar Enugu ta tasa ƙeyar wani tsoho mai shekaru 70, Anthony Mgbe zuwa gidan yari bisa zargin laifin kashe wata yarinya ‘yar shekara 15. Wanda aka kashen mai suna Uchechukwu Onwuzuru, wanda aka ce kurma ce kuma bebiya, ta zubar da jini har ta mutu bayan da wanda ake zargin…
-
An yi wa budurwar da ta yi tatil da giya fyaɗe a Ogun
’Yan sanda a jihar Ogun sun kama wani mai suna Gbenga Kolawole bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekara 16 fyaɗe bayan ta yi tatil da giya. Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru da budurwar ne yayin wani taron cika shekara bakwai da wani coci ya shirya a Adubi da ke jihar ranar…
-
Mahaifi ya yi wa ’yar cikinsa mai shekara 13 fyaɗe
Wani mahaifi mai shekara 42 mai suna Babatunde Afolayan, ya faɗa komar jami’an ’yan sanda a Jihar Legas, bisa zarginsa da shafe tsawon shekara uku yana yi wa ’yar cikinsa fyaɗe. Aminiya ta rawaito cewa mutumin, wanda mazaunin unguwar Ikorodu ne da ke Jihar ta Legas, ya riƙa yi wa ɗiyar tasa fyaɗe tun tana shekara 10…