Burtaniya ta tisa ƙeyar ‘yan Najeriya da Ghana 44 zuwa gida

0
17
Burtaniya ta tisa ƙeyar 'yan Najeriya da Ghana 44 zuwa gida

Burtaniya ta tisa ƙeyar ‘yan Najeriya da Ghana 44 zuwa gida

‘Yan Najeriya da wasu ‘yan ƙasar Ghana kimanin arba’in da huɗu aka mayar ƙasashen su na asali bayan da aka samesu da laifin zama ba bisa ƙa’ida ba a Burtaniya.

Jaridar Guardian da ake bugawa a kasar ta Birtaniya ta bayyana damuwa a game da yanayin da ta ce ta sami ‘yan ciranin da suka shigo kasar neman rayuwa mai inganci a gabanin a mayar da su kasashensu, inda ta tattauna da wani da yayi yunkurin halaka kansa da wani da ya bayyana cewa ya zauna a Ingila na tsawon shekaru 15, amma duk da haka ba a amince da shaidar neman mafakarsa ba, lamarin da ya bayyana a matsayin tsagwaron rashin adalci.

KU KUMA KARANTA:Ana tuhumar wani ɗan Najeriya kan hana mata kai ƙarar mazajensu wajen ‘yansanda

Tun bayan da jam’iyyar Labour ta hau karagar mulki a watan Yulin da ya gabata, an fitar da ‘yan cirani kimanin dubu uku da dari shida da suka fito daga kasashe daban-daban bayan da yunkurinsu na neman mafaka ya ci tura.

Gwamnatin Britaniyan dai ta sha alwashin ci gaba da korar bakin da suka zame mata alakakai a kasa.

Leave a Reply