Budurwa ‘Yar IPOB da ta ƙware a kisan mutane ta shiga hannu

Hukumar leƙen asiri ta Eons ta fitar da hotunan da ke nuni da lokacin da jami’an tsaron Najeriya suka kama Amaka Onah, ‘yar shekara 22 ‘yar ƙungiyar IPOB/ESN a ƙaramar hukumar Igboeze ta Kudu, a Nsukka, jihar Enugu.

Ramukan da suke binne mutane

Waɗanda ake zargin ta amsa cewa sun kashe aƙalla mutane 5 ciki har da Igwe Baniko ɗaya wanda suka ƙone masa gidan mai.

Ta kuma bayyana cewa wan mai suna Duri da ke hannun jami’an tsaro a halin yanzu shi ne yake shugabantar aikin nasu.

Budurwar ta kuma jagoranci jami’an tsaro zuwa ga ramukan da suke binne mutanen da suka kashe.


Comments

2 responses to “Budurwa ‘Yar IPOB da ta ƙware a kisan mutane ta shiga hannu”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Budurwa ‘Yar IPOB da ta ƙware a kisan mutane ta shiga hannu […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Budurwa ‘Yar IPOB da ta ƙware a kisan mutane ta shiga hannu […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *