Hukumar Kula da Matasa Masu yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) ta fara ba da horo ga matasa masu yi wa ƙasa hidima su 1,161 a sansanin horar da malamai na ATC da ke Jihar Borno.
Kimanin shekaru 12 ke nan sansanin ya shafe a rufe sakamakon ta’addancin Boko Haram.
Fara horarwar wanda aka shirya yi a ranar Juma’a mai zuwa a Maiduguri, zai gudana ne a sansanin mai ɗaukar mutane 3,000.
Shugaban hukumar a jihar, Mohammed Adamu, ya ce, “Sojoji, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro sun tabbatar mana da tsaron jami’anmu, da jami’an wayar da kan jama’a da kuma jami’an hukumar da ke wannan sansani da aka gyara.”
Ya yi nuni da cewa, an dawo da shirin ne bayan shekaru 12 da Boko Haram ta fara ta’addanci a jihar kamar yadda aka ambata a baya.
KU KUMA KARANTA: Hukumar NYSC ta musanta tura membobin ƙungiyar zuwa jamhuriyar Nijar
Dangane da dabarun da sansanin yake da shi, ya ce: “Sansanin ATC na gwamnatin jihar da aka gyara yana tsakiyar ofisoshin hukumomin tsaro da ke kan titin filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Janar Muhammadu Buhari a Maiduguri.”
Don haka ya kawar da duk wata fargabar da iyaye da masu kula da su ke da ita ta kare lafiyar ’ya’yansu a lokacin da za su karɓi horo na mako uku.
Ya ƙara da cewa mazauna Maiduguri da suka haɗa da Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn El-Kanemi, sun cika maƙil da farin ciki kan yadda za a dawo da horar da matasan a Jihar.
Da yake duba sansanin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mohammed Yusuf, ya ce, “Maƙasudin ziyararmu ita ce duba yanayin tsaro a yankin, tare da sanin haƙiƙanin yadda aka tura jami’an tsaro.”
Don haka, Kwamishinan ya ba da tabbacin tura isassun jami’an ’yan sanda a wuraren shiga da fita sansanin, gami da muhimman wurare na tsaro.
[…] KU KUMA KARANTA: Bayan shekara 12 da rufe sansanin NYSC a Borno, an sake buɗe shi […]
[…] KU KUMA KARANTA: Bayan shekara 12 da rufe sansanin NYSC a Borno, an sake buɗe shi […]