Bana neman takarar shugaban ƙasa – Ganduje

0
95
Bana neman takarar shugaban ƙasa - Ganduje

Bana neman takarar shugaban ƙasa – Ganduje

Shugaban riƙo na jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje ya yi zargin cewa ‘yan Kwankwasiyya ne suka buga fastocinsa da ke nuna cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

A wata sanarwa da Edwin Olofu, mai magana da yawun Ganduje ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya yi watsi da fastocin da aka mammanna a wasu yankuna na ƙasar, musamman a Babban Birnin Tarayya da ke nuna shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa tare da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, a matsayin mataimakinsa.

Sanarwar ta ce, “Muna sanar da jama’a cewa fastocin da a yanzu haka ake watsawa a shafukan sada zumunta, waɗanda ke iƙirarin cewa shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje, zai yi takarar shugaban ƙasa a 2027 tare da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, a matsayin mataimakinsa, ƙarya ce tsagwaronta kuma labari ne na ƙanzon kurege.

KU KUMA KARANTA: Ɗan takarar kansila na AAC ya ka da na jam’iyya mai mulki PDP a Bauchi

“Jam’iyyar All Progressives Congress tana so ta bayyana ƙarara cewa wannan aiki ne na maƙetata, da wataƙila suka haɗa baki da wasu ‘yan Kwankwasiyya, waɗanda suka sha alwashin haddasa rashin jituwa tsakanin Dr. Ganduje da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu,” in ji sanarwar.

Sai dai sanarwar ba ta bayar da wata hujja da ke nuna cewa ‘yan Kwankwasiyya ne suka buga fastocin da ke nuna Ganduje a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ba.

Kazalika kawo yanzu ‘yan Kwankwasiyya ba su yi raddi kan wannan zargi ba.

Leave a Reply