Ban Amince Da Hukuncin Majalisar Gudanarwar KadPoly A Kaina Ba – Farfesa Sani Yahaya

0
286

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WANI Malami a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Farfesa Mohammed Sani Yahaya, ya kalubanci Majalisar Gudanarwar ta Jami’ar Fasaha da kere-kere ta tarayya dake Jihar Kaduna, (Kaduna Polytechnic) ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, bisa zargin kin bin dokar tsarin daukar shugabancin Jami’ar.

A wata takardar da ya tabawa manema labarai a wani taron da aka gudanar, a sakatariyar kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya reshen Jihar Kaduna, Farfesa Yahaya ya bayyana rashin amincewarsa bisa irin tsarin da Majalisar Gudanarwar ta yi na kin bashi dama kasancewarsa tsohon malami wanda ya dade a Jami’ar.

A cewar mai shigar da karar wanda ya kalubanci Majalisar Gudanarwar, ya nemi mukamin shugabancin Jami’ar ne wato (Rector), kuma an kore shi ne bisa dalilin cewa shi yanzu Farfesa ne da ke koyarwa a wata Jami’ar.

Farfesa Yahaya Malami a Sashen Kimiyyar amfanin gona na tsangayar noma, a cikin takardar koke da aka rubuta ranar 20 ga watan Janairu, 2022 yana neman majalisar gudanarwar Jami’ar Tarayyar dake Kaduna, da ta sake nazari tare da soke hukuncin da ta yanke domin tabbatar da adalci, gaskiya da bin doka.

Mai shigar da karar, ya goyi bayan ikirarin nasa da takardu domin kalubalantar hukuncin da Majalisar ta yanke, inda ya ce ya kamata Majalisar Gudanarwar ta sake duba matakin da ta dauka domin ya saba wa dokar Jami’ar ta shekarar 2019.

Ya bayyana cewa, ya rubuta takarda kai tsaye ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufai, da Mai Martaba Sarkin Zazzau, da Mai Girma Ministan Ilimi, Mai Girma Ministan Shari’a, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai. Manyan Jami’o’i da TETFUND, Shugaban Kwamitin Majalisa kan Ilimi da Aiyuka da Sakatariyar Zartarwa, Hukumar Ilimin Fasaha ta Kasa da sauran masu fada a ji da zummar ya bukace su ja hankalin Majalisar Jami’ar don ta gyara kura-kuran ta.

Farfesa Mohammed Sani kwararre ne a fannin noman rani kuma tsohon shugaban sashin kimiyyar amfanin gona na tsangayar aikin gona ne na Jami’ar jihar Kaduna.

Leave a Reply