Babu wutar lantarki, babu ƙuri’ar ‘yan Najeriya a 2027 – Obi ga Tinubu 

0
310
Babu wutar lantarki, babu ƙuri'ar 'yan Najeriya a 2027 - Obi ga Tinubu 
Obi da Tinubu

Babu wutar lantarki, babu ƙuri’ar ‘yan Najeriya a 2027 – Obi ga Tinubu

Daga Jameel Lawan Yakasai

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Mista Peter Obi, ya yi ba’a ga Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC bayan sake lalacewar Babban layin wutar lantarki na ƙasa, wanda ya jefa Najeriya cikin duhu.

Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, ya tunatar da alƙawarin da Tinubu ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe cewa idan bai samar da wutar lantarki mai dorewa cikin shekaru huɗu ba, kada a sake zaɓar shi wa’adi na biyu.

A cikin wata sanarwa mai taken “Idan ban ba ku wutar lantarki mai dorewa a cikin shekaru 4 masu zuwa ba, kada ku zaɓe ni wa’adi na biyu”, Obi ya ce:

“Alƙawarin ya yi ƙarfi matuƙa har ba zai yiwu ’yan Najeriya su manta da shi ba, musamman yadda Shugaban ƙasa ya faɗi a ranar 22 ga Disamba, 2022 cewa: ‘Idan ban samar muku da wutar lantarki mai dorewa cikin shekaru 4 ba, kada ku zaɓe ni wa’adi na biyu.’”

KU KUMA KARANTA: Magoya bayana su zaɓi jam’iyar ADC a zaɓukan cike-gurbi – Peter Obi

Ya bayyana cewa gwamnatin APC ta jagoranci rushewar tsarin wutar lantarki na ƙasa fiye da kowace gwamnati a tarihin Najeriya, duk da biliyoyin dalolin da aka zuba a fannin makamashi.

Yayin kwatanta Najeriya da wasu ƙasashe masu tasowa, Obi ya ce: “Najeriya ta kashe kuɗi da yawa wajen samar da wutar lantarki fiye da ƙasashen Vietnam, Masar, Indonesia da Bangladesh, amma babu wani ci gaba a samarwa. Su sun ƙara dubban megawatts, amma Najeriya ta tsaya daga 4,500MW zuwa kusan 5,000MW kawai.”

Leave a Reply