Australia ta goyi bayan ƙudurin MƊD na tsagaita wuta a Gaza

0
194

Ministar harkokin wajen Australia Penny Wong, ta ce ƙasar ta goyi bayan wani ƙuduri na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya buƙaci a tsagaita wuta a Zirin Gaza, saboda nuna damuwa ga fararen hula a yankin da aka yi wa ƙawanya, a wani ra’ayi da ya jawo rabuwar kai da babbar ƙawarta Amurka.

Bayan gargaɗin da jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya suka yi game da ta’azzarar ƙazamin rikicin jinƙai a Gaza a yaƙin da Isra’ila ta kwashe watanni biyu ana yi a can, MƊD mai wakilai 193 ta amince da ƙudurin tsagaita wuta inda ƙasashe 153 da suka haɗa da Australia suka kaɗa ƙuri’ar amincewa da tsagaita wutar, inda 23 kuma suka ƙaurace wa kaɗa ƙuri’ar.

Ƙasashe goma ne suka kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa da tsagaita wutar kuma sun haɗa da Amurka da Isra’ila.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila da Hamas sun amince a kara wa’adin tsagaita wuta da kwanaki bakwai

Wong ya shaida wa wani taron manema labarai a Adelaide bayan da MDD ta zartar da ƙudirin cewa, Australia ta ci gaba da tabbatar da hakkin Isra’ila na kare kanta. “Kuma a yin haka, mun ce dole ne Isra’ila ta mutunta dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, dole ne a kare fararen hula da kayayyakin aikin farar hula, ciki har da asibitoci.

“Ƙudurin da muka goyi bayan ya yi daidai da matsayin da muka zayyana a baya kan wadannan batutuwa.”

Leave a Reply