Atiku ya buƙaci a bawa ‘yan ƙasa damar zaɓar shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC tare da kwamishinoninsa
Daga Jameel Lawan Yakasai
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya nemi a bai wa ‘yan Najeriya damar zaɓen shugaban Hukumar Zabe INEC da Kwamishinoninta kai tsaye.
Ya ce hakan zai taimaka wajen dawo da sahihancin zaɓe, ganin cewa zaɓen 2023 da ya gabata ya samu mafi ƙarancin halartar jama’a zuwa runfunan zabe.
KU KUMA KARANTA: Ni ban matsa dole sai na zama shugaban ƙasa ba – Atiku
Atiku ya kuma bukaci a sanya dokar da za ta tilasta amfani da katin BVAS da kuma tura sakamakon zaɓe ta kafar intanet, domin kaucewa rashin gaskiya da dogaro da kotu.
Ya ja hankalin cewa, idan ba a yi waɗannan gyare-gyaren ba, za a ci gaba da ganin jama’a na ƙin fita kada kuri’a, abin da zai barazana ga dimokuraɗiyya a ƙasar nan.









