Atiku da Obi sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli don ta soke nasarar Tinubu

0
273

Daga Ibraheem El-Tafseer

‘Yan takarar na manyan jam’iyyun adawar Najeriya, Atiku Abubakar na PDP da takwaransa Peter Obi na Labour Party sun garzaya gaban Kotun Ƙolin ƙasar don ƙalubalantar hukuncin Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, wadda ta kori ƙararrakin da suka shigar a kan nasarar zaɓen Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.

Ayarin alƙalai guda biyar ne a ranar 6 ga watan Satumba, suka yanke hukuncin bai ɗaya na cewa duk ‘yan takarar jam’iyyun adawa sun gaza tabbatar da hujjar cewa zaɓen yana cike da kura-kurai.

Sun ayyana cewa masu ƙorafin ba su iya tabbatar da zarge-zargen aringizon ƙuri’u ba, da take ‘yancin masu zaɓe, kuma sun gaza kawo isassun shaidu da za su tabbatar da ƙararrakinsu.

Da yake ƙalubalantar hukuncin, ɗan takarar PDP Atiku Abubakar ya nemi Kotun Ƙoli ta soke hukuncin kotun zaɓen shugaban ƙasa, inda ya nunar cewa hukuncin da ya tabbatar da nasarar zaɓen Tinubu “cike yake da manyan kura-kurai da kuma rashin adalci”.

KU KUMA KARANTA: Ranar Laraba kotun ƙolin Kano za ta yanke hukunci kan zaɓen Gwamna a jihar

Babban ɗan adawar na Najeriya ta hannun lauyansa, ya kuma soki yadda kotun ta yi amfani da “kalaman aibatawa” waɗanda ya ce, “sun nuna fifita wani ɓangare”.

A wani mataki makamancin wannan, Peter Obi na jam’iyyar Labour ya nunar cewa kotun zaɓen shugaban ƙasa ta kawar da kai ga gaskiyar al’amuran da ya gabatar a shari’arsa, kuma ta gaza yin la’akari da girman shaidun da ya gabatar, abin da ya sa ta kai ga hukunci mai cike da kuskure.

Lauyoyin masu ƙorafin a ranar Talata sun shigar da sanarwar ɗaukaka ƙararrakinsu a kan dalilai masu yawa, ciki har da batun cewa kamata ya yi Kotun Ƙoli ta jingine hukuncin ƙaramar kotu, wanda ya tabbatar da nasarar Bola Tinubu, kuma ta ayyana cewa bai cancanci tsayawa takarar shugaban ƙasa a Najeriya ba a lokacin da ya yi hakan.

A cewarsu, bisa hujjar an taɓa kama shi da laifi kan zargin safarar ƙwaya a Amurka.

Ba a dai sanya wata rana don sauraron shari’o’in ba.

Kuma har yanzu jam’iyyar APC mai mulki ba ta ce uffan kan wannan sabon mataki ba, mako biyu bayan murnar samun nasara kan hukuncin da ya tabbatar da zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

Leave a Reply