Asusun TETFund ya samu Tiriliyan 1.6 don tallafa wa makarantun gaba da sakandare

0
140
Asusun TETFund ya samu Tiriliyan 1.6 don tallafa wa makarantun gaba da sakandare

Asusun TETFund ya samu Tiriliyan 1.6 don tallafa wa makarantun gaba da sakandare

Daga Jameel Lawan Yakasai

Asusun tallafin Ilimi na manyan makarantun gaba da sakandire (TETFund) ya bayyana cewa ya karɓi kuɗin Naira tiriliyan 1.6 domin gudanar da ayyuka daban-daban a makarantun gaba da sakandare dake fadin Najeriya.

Shugaban Hukumar TETFund kuma tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Masari, ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da manema labarai a Katsina ranar Lahadi. Ya ce wannan kuɗin ya samu ne daga harajin kashi uku cikin ɗari na ribar kamfanoni kamar yadda dokar TETFund ta tanada.

KU KUMA KARANTA: An ƙaddamar da littattafai 50 da TETFund ta ɗauki nauyin bugawa a Hediƙwatarta dake Abuja

Masari ya ƙara da cewa kashi 40 cikin ɗari na wannan kuɗi, wato Naira biliyan 460, za a ware shi ne don tallafi ga makarantun gaba da sakandare a duk faɗin Najeriya. A matakin jihohi, an zaɓi makaranta guda uku a kowace jiha, jami’a ɗaya, polytechnic ɗaya, da kwalejin ilimi ɗaya, waɗanda za su amfana da tallafin.

Haka kuma, TETFund ta bayar da Naira biliyan 225 ga Hukumar Lamunin Ilimi ta Najeriya (NELFUND) don tallafawa shirin lamunin ɗalibai na gwamnatin tarayya.

KU KUMA KARANTA: TETFUND ta yi alƙawarin magance matsalar ambaliyar ruwa a jami’ar jihar Jigawa

Bugu da ƙari, an ware Naira biliyan 70 don tallafawa samar da wutar lantarki ta hasken rana ko iskar gas a makarantun gaba da sakandare, sannan an kuma ware Naira biliyan 25 domin inganta tsaro a cikin kwalejoji da jami’o’i ta hanyar samar da fitilun titi da sauran kayan tsaro.

Masari ya ce TETFund ta kashe sama da Naira biliyan 100 wajen karfafa horon kimiyyar lafiya a makarantun gaba da sakandare, domin ƙara yawan ƙwararrun likitoci, ma’aikatan jinya, magunguna da sauran ma’aikatan lafiya. Wannan mataki na cikin shirin shugaban ƙasa Bola Tinubu na magance karancin ma’aikatan lafiya a ƙasar.

Leave a Reply