APGA ta lashe kujerar Sanatan Anambra ta Kudu a zaɓen cike-gurbi

0
173
APGA ta lashe kujerar Sanatan Anambra ta Kudu a zaɓen cike-gurbi

APGA ta lashe kujerar Sanatan Anambra ta Kudu a zaɓen cike-gurbi

Jam’iyyar APGA ta lashe zaɓen cike-gurbi na kujerar Sanatan Anambra ta Kudu da kuma na majalisar dokokin jihar a mazabar Onitsha ta Arewa, da aka gudanar ranar Asabar.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ce ta sanar da sakamakon zaɓukan guda biyu a safiyar yau Lahadi a kananan hukumomin Onitsha da Nnewi.

A ofishin INEC na Nnewi, jami’in tattara sakamakon zaɓe, Farfesa Frank Ojiako, ya bayyana Cif Emmanuel Nwachukwu na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe kujerar Sanatan Anambra ta Kudu.

Nwachukwu ya samu ƙuri’u 90,408 inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Cif Azuka Okwuosa na jam’iyyar APC, wanda ya samu ƙuri’u 19,847.

KU KUMA KARANTA: Jam’iyar PDP ta yi kira ga hukumar zaɓe ta ƙasa, da a soke zaɓen cike-gurbi da aka yi a Kano 

Donald Amangbo na jam’iyyar ADC ya zo na uku da ƙuri’u 2,889.

Haka zalika, INEC ta bayyana Ifeoma Azikiwe na jam’iyyar APGA a matsayin wadda ta lashe kujerar majalisar dokokin jihar a mazabar Onitsha ta Arewa 1.

A yayin bayyana sakamakon a Onitsha, jami’in tattara sakamakon, Farfesa Ibiam Ekpe, ya ce Azikiwe ta samu ƙuri’u 7,774 inda ta doke babban abokin hamayyarta, Justina Azuka na jam’iyyar ADC, wadda ta samu ƙuri’u 1,909.

Ɗan takarar APC, Ezennia Ojekwe, ya samu ƙuri’u 1,371 yayin da ɗan jam’iyyar YPP, Njideka Ndiwe, ya samu ƙuri’u 655.

Leave a Reply