APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Kashim Shettima a zaɓen 2027
Jam’iyyar APC, ta musanta jita-jitar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na shirin sauya Mataimakinsa, Kashim Shettima, kafin zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce babu wata matsala tsakaninsu kuma maganar sauya Shettima ba ta da tushe.
Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Bala Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa wasu ne ke yaɗa wannan jita-jitar don tayar da ƙura.
Wannan jita-jita ce kawai marar tushe. Maganganu ne da bai kamata a ɗauke su da muhimmanci ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Ko da a ce akwai wani dalili da zai sa shugaban ƙasa ya sauya mataimakinsa, ba zai iya yin hakan shi kaɗai ba. Dole sai da shawarwari tare da masu ruwa da tsaki.”
Ko da yake APC ba ta bayyana aniyar Tinubu na sake yin takara a karo na biyu ba, magoya bayansa da wasu shugabannin jam’iyya sun fara neman goyon baya don ya sake tsayawa takara a 2027.
Wasu na ganin ya cancanci ya nemi wa’adi na biyu domin kammala ayyukan da ya fara.
A halin yanzu, wasu ’yan siyasa daga yankin Arewa ta Tsakiya suna kira da a ba su tikitin shugaban ƙasa ko mataimaki a zaɓe mai zuwa.
KU KUMA KARANTA:Ban yanki jiki na faɗi ba, ƙarya aka yi mi ni — Wike
Sun ce tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, yankin bai taɓa samun shugaba ko mataimakin shugaban ƙasa ba.
Farfesa Nghargbu K’tso, wanda ya wakilci tawagar, ya ce: “Daga cikin yankuna shida na ƙasar nan, Arewa ta Tsakiya da Kudu Maso Gabas ne kaɗai ba su taɓa samar da shugaban ƙasa ko mataimaki ba cikin shekaru 26 da suka gabata. Lokaci ya yi da za a yi adalci da haɗin kai.”
Sai dai Bala Ibrahim, ya mayar da martani cewa buƙatar Arewa ta Tsakiya ba ta da tushe kuma “ta mutu tun kafin ta fara.”
Ya ce yankin bai taka gagarumar rawa a zaɓen da ya gabata ba bare ya nemi irin wannan buƙata, kuma ba yanzu ne lokacin tattauna rabon muƙamai ba, tunda Tinubu bai kammala wa’adinsa na farko ba.