Anfanin ganyen magarya ga lafiyar Ɗan Adam
Itaciyar magarya wadda akafi sani da (Assidir) a larabce kuma (Lote) a turance, itaciyace mai albarkatun da daɗewa, Annabi S.A.W ya tabbatar da amfaninsa.
Magarya yana ƙunshe da magunguna masu matuƙar mahimmanci ga jikin ɗan Adam kuma yana da ƙarfin kashe ƙwayoyin cuta cikin dan ƙanƙanin lokaci.
Magarya Antibiotic ne mai ƙarfin gaske kuma cikin ikon Allah bashi da wani illa wato “side effects” na azo agani.
KAƊAN DAGA CIKIN AMFANINTA
1. Ciwon daji (cancer) :
Idan ana dafa garin magarya ana sha da zuma yana kashe ƙwayar cutar daji koda a cikin jini ne idan kuma ya yi miki sai arinka dafa garin magaryar da ruwan khal ana wanke wurin mikin idan an wanke sai a barbaɗa garin magaryar.
2. Yana da ƙarfin yaƙar cutar fata kamar su tautau, makero, ƙazuwa da sauransu.
A kwaɓa shi da zuma a rinka sha ana shafawa a wurin da abin ya shafa.
3. Yana tsaftace jini domin yana ɗauke da sinadarin Saponin, alkaloid da triterpenoid waɗannan sinadarai ne masu tsaftace jini.
4. Shansa da ruwan zafi yana magance gajiya da ciwon Jiki.
5. Yana magance ulcer idan ana shansa da madara ko zuma.
KU KUMA KARANTA: Anfanin ayaba 12 da ya haɗar da kiyaye lafiyar ƙoda, anfani ga mata masu juna biyu, da taimakawa ƙwaƙwalwar ɗalibai
6. Yana taimakawa hanta ya hana shi jin ciwo da cututtuka.
7. Yana daidaita nauyin mutun.
8. Yana tsaida zawo cikin ƙanƙanin lokaci idan aka shashi da ruwa ko koko.
9. Yana miƙar da kasusuwa musamman gamai karaya.
10. Yana maganin rashin sha’awa ga mata idan suna tsarki dashi kuma suna shansa da madara.
11. Kuma a ƙarshe dai yana warware sihiri a cewar malaman sunna idan aka jiƙa garin a ruwa tare da karanta wasu ayoyi daga cikin Alqur’ani mai girma.
Allah yasa mu dace.