No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani jami’in Kwastam mai suna Abdulwahab Magaji, ana zargin ya harbi kansa ne da bindiga ƙirar Pump Action a gidansa da ke Rukunin Gidajen Farm Estate da ke layin Binta Street a Abuja.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa iyalan marigayin mai muƙamin CSC da ke aiki a Abuja ne dai suka sanar da ’yansanda cewa ya harbi kansa da bindigarsa a gida.

Bayan isowar ’yansanda ne aka ɗauke shi jina-jina zuwa asibiti inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

An ba da gawar mamacin ga iyalansa, domin a yi mata jana’iza bisa Koyarwar addinin Musulunci.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama wani mutum bisa zargin kashe abokinsa da sace motarsa a Kano

Neptune Hausa ta tuntuɓi kakakin hukumar kwastam na ƙasa, Abdullahi Maiwada, inda ya tabbatar mana da faruwar lamarin, ya ce “an tabbatar da mutuwarsa, amma babu tabbacin ko shi ne ya kashe kansa, ko kuma kashe shi aka yi”. Sai dai ‘yansanda suna bincike don gano haƙiƙanin yadda ya mutu.

Wani abokin marigayin, mai suna Lawan Al-Amin Mohammed, ya tabbatar da rasuwar CSC Magaji, wanda ya bayyana a matsayin jajirtacce, mutumin kirki mai riƙon amana kuma mai taimakon jama’a a lokacin rayuwarsa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...