Ana zargin tsohon firaiministan Sudan Hamdok da laifin ‘tunzura’ mutane su yi yaƙi

0
149

Ofishin mai shigar da ƙara na Sudan ya zargi tsohon firaiministan ƙasar Abdalla Hamdok da laifin “tunzura” mutane domin su “yaƙi ƙasar” da kuma wasu laifuka da ka iya sanyawa a yanke wa mutum hukuncin kisa, a cewar gidan talbijin na ƙasar

Ofishin mai shigar da karar yana biyayya ga shugaban mulkin soji Janar Abdel Fattah al Burhan, wanda tun watan Afrilun 2023 dakarunsa suke gwabza yaƙi da na mataimakinsa kuma shugaban dakarun sa-kai na RSF, Mohamed Hamdan Dagalo.

Mutane goma sha biyar, ciki har da ƴan jarida da ƴan siyasa, waɗanda su ma suke zaune a ƙasashen waje, suna fuskantar irin wannan zargi na “keta kundin tsarin mulki”.

KU KUMA KARANTA: Sudan ta Kudu za ta rufe duka makarantun ƙasar saboda tsananin zafi

Hamdok, wanda shi ne ɗan siyasa farar-hula mafi shahara a Sudan, ya rike muƙamin firaiministan ƙasar bayan tumɓuke gwamnatin Omar al Bashir.

A wata Oktoba na 2021 aka yi wa Hamdok ɗaurin-talala bayan juyin mulkin da Dagalo da Burhan suka yi lokacin suna ɗasawa da juna.

Amma an saki Hamdok kuma a watan Janairun 2022 ya ajiye muƙaminsa sannan ya fice daga ƙasar zuwa Abu Dhabi. Tun daga wancan lokaci ne ya shiga cikin wata gamayya mai suna Taqadum.

Yaƙin Sudan ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba mutum miliyan 8.5 da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Leave a Reply