Ana zargin ‘ma’auratan bogi’ da ɓoye hodar-ibilis a al’aura

0
202

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) sun kama wasu mutum biyu, da suka yi ƙaryar cewa ma’aurata ne da ke da niyyar zuwa Indiya domin rashin lafiya da hodar-ibilis.

Mutanen biyu Mista Ilonzeh Kingsley Onyebuchi da Misis Ilonzeh Roseline Nonyelum, an kama su ne da ƙulli 184 na hodar-ibilis da nauyinta ya kai kiligiram 3.322, an kuma gano wata ƙwayar mai nauyin giram 100 ɓoye a ɗan kamfan matar.

Jami’an NDLEA sun kama mutanen biyu a wurin binciken kayayyaki na farko a filin jirgin sama na Legas, a lokacin da suke ƙoƙarin shigar jirgi zuwa Indiya.

Duk da cewa sunayen da ke jikin takardun tafiyarsu ya nuna cewa ma’aurata ne, hukumar NDLEA ta buƙaci ɗauki hoton jikinsu.

Hoton da ya tabbatar da cewa akwai hodar-ibilis ɗin a jikin nasu, a don haka ne jami’an hukumar suka kai wa wani ɗakin gwaji domin tilasta musu fito da abin da suka ɓoye a jikin nasu.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NDLEA ta kama ɗan kudancin ƙasar Amurka, ɗauke da hodar Iblis

Yayin da sunayen da ke jikin takardun tafiyarsu ya nuna suna iri ɗaya, wato Ilonzeh Kingsley Onyebuchi ga manijin, da matar Ilonzeh Roseline Nonyelum, binciken farko da hukumar ta gudanar ya gano cewa mutanen ba ma’aurata ba ne.

Binciken ya nuna cewa sun yi amfani da suna ɗaya domin kawar da hankalin jami’an tsaro a wajen bincike.

Sunan matar na gaskiya shi ne Ngogbike Nkechi kamar yadda bincken ya bayyana.

Leave a Reply