Ana zargin Fulani makiyaya da kai harin ramuwar gayya a wasu ƙauyuka a Yobe

0
216

Daga Ibraheem El-Tafseer

Al’ummar ƙauyukan Gurjaje da Malari da ke ƙaramar hukumar Fika ta jihar Yobe sun shiga cikin ruɗani bayan da ake zargin Fulani makiyaya ne suka mamaye ƙauyukansu a ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa makiyayan da suka kai harin ramuwar gayya ga mutanen ƙauyen biyo bayan wani yunƙuri da al’ummar yankin suka yi a lokacin da shanun Fulani suka mamaye gonakinsu na kankana.

Zagazola Makama ƙwararre a fannin yaƙi da tada ƙayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya samu labarin cewa makiyayan sun auka wa al’ummar ne a kan babura inda galibinsu ɗauke da Kwari-da-baka da kibau, inda suka yi jerin gwano.

Ko da yake har yanzu ba a tabbatar da asarar rayuka ba, makiyayan sun yi nasarar ƙona gidaje da dama a yankin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe ‘yansanda da garkuwa da mutane 40 a Zamfara

Majiyoyi sun ce rikicin da makiyayan suka fara yi tsakanin makiyaya da manoma a yankunan ya faru ne a watan Janairu lokacin da shanun suka lalata gonakin kankana.

An tattaro cewa makiyayan da suka yi iƙirarin cewa manoman sun sace wasu shanunsu sun sha alwashin koya wa ɗaukar ramuwar gayya akan su.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a kama su ba, kuma manoman da ke cikin ruɗani na ƙirga asarar da suka yi.

Leave a Reply