Ana tuhumar wani ɗan Najeriya kan hana mata kai ƙarar mazajensu wajen ‘yansanda

0
66
Ana tuhumar wani ɗan Najeriya kan hana mata kai ƙarar mazajensu wajen ‘yansanda

Ana tuhumar wani ɗan Najeriya kan hana mata kai ƙarar mazajensu wajen ‘yansanda

A cikin bidiyon da jaridar UK Mirror ta ruwaito an ga ɗansandan yana magana cikin harshen Yarbanci, ɗaya daga cikin manyan harsunan da ake amfani da su a Najeriya.

Wani faifayin bidiyo da ake ta yaɗa wa a yanar gizo ya nuna yadda ake zargin wani ɗansandan Birtaniya da laifin faɗawa matan Najeriya da su riƙa lallaɓa auren su.

Ɗansandan ya kuma nemi da su guji kai ƙarar mazajensu wurin ‘yansanda wanda a halin yanzu ake gudanar da bincike akan shi bayan da aka fara yaɗa bidiyon kuma a kafafen sada zumunta bayan shekaru 6.

A cikin bidiyon da aka dauka a wata majami’a mai suna Divine Restoration International Church a Camberwell a shekarar 2018 ya nuna wani jami’in ‘yan sandan yana yi wa wani taron mata jawabi yayin da wasu ‘yan sanda uku daga kungiyoyin kare hakkin mutanen da aka zalunta da suke tsaye a gefe suke ta bayyana bacin ransu.

A cikin bidiyon da jaridar UK Mirror ta ruwaito an ga dan sandan yana magana cikin harshen Yarbanci, daya daga cikin manyan harsunan da ake amfani da su a Najeriya, da kuma harshen turanci yayin da yake tsaye akan mimbari inda yake wa’azi akan aikata laifuka da wuka da kuma yadda ‘yaya maza ba za su yi wa iyayensu mata biyayya ba kamar yadda za su yi wa iyaye maza.

Derbie ta ce ran ta ya baci sosai a lokacin da ta kalli bidiyon.

A cikin bidiyon, jami’in ya ci gaba da cewa, da zarar matan Najeriya suka isa Birtaniya, sai dabi’unsu su sauya su fara yi wa mazan su rashin kunya, sannan ya kara da cewa kada su kirawa mazan nasu ‘yan sanda, amma su yi hakuri su jure.”

‘Yan sandan sun kuma tabbatarwa jaridar UK Mirror cewa an ja hankalin sashin ‘yan sandan da ke bibiyar al’amuran da’a akan faifayin bidiyon.

KU KUMA KARANTA:Ɗan Najeriya mazaunin Burtaniya ya ƙirƙiro fasahar AI don gano maɓoyar ‘yan fashi

Cikin wata wasikar kara, kungiyar “Children Safeguarding Group Africa, ta bayyana bacin rai akan wannan furucin.

A hirar ta da UK Mirror, jagorarar kungiyar ta Affika Derbbie Ariyo, wace ita ma ta kalli bidiyon, ta ce “abin da Jami’in ya fada shine “kada ku kai karar mazan ku gun ‘yan sanda, ku yi hakuri ku lallaba.”

Su ma sauran Jami’an ‘yan sandan da ke tare da shi a yayin da yake yiwa wannan furucin da yake yiwa wasu mata nasiha shi ma yanzu ana tuhumar shi.

Shugabar kungiyar ta ce”Na yi fushi da na ji zancen. Rai nan a ya baci sossai. Wai ma me kake nufi ne? Yanzu idan aka ce wani yana cin zarafin matasrsa, sai tayi shuru? Kada fa ku manta, cin zarafi ya kunshi abubuwa da dama ba yana nufin cewa yana mata duka ne kawai ba, ko da a al’adance ne sai mace tayi shuru ta ki yin Magana don tana tsoro mijin ta zai kore ta daga gidan yaran kuma su shiga garari kuma a baya duk a dora mata laifinakan ta.

Ace wai idan ana zaluntar mace sai ta ki neman kariya ko taimakon ‘yan sanda? Ta kuma kara da cewa gaskiya abinda suka yi bai dace ba, kuma tamkar kamar sun ma mai da matsalar cin zarafi a cikin al’ummar mu ya zama ba komai ba kawai.

Shugabar kungiyar ta kuma bayyana cewa, yara ma basu tsira ba daga matsalar cin zarafi a cikin gida.

Ta kuma bayyana cewa tana gani cewa ba a mai da hanaklai akan matsalar cin zarafi a cikin al’umma sakamakon cewa aklaluman hukumar ‘yan sanda da suka aikawa kamfanin dillancin labaran PA ya nuna cewa hukumar ‘yan sandan samu rahoton cin zarafin mata 21 a 2022 kuma kaso 43% daga cikin su duk mata ne bakaken fata wanda alkaluman su ya zarta na sauran al’ummomi.

Leave a Reply