Ana ta ƙara gwabza faɗa a Sudan ‘yan sa’o’i kaɗan kafin yarjejeniyar tsagaita wuta

2
297

Ana ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa a babban birnin ƙasar Sudan, Khartoum, ‘yan sa’o’i kaɗan kafin yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta ta fara aiki a yammacin ranar Litinin.

Kafofin yaɗa labaran cikin gida sun ruwaito cewa ana jin ƙarar harbe-harbe da safe. Tun da farko a ranar Asabar, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana cewa, wakilan sojojin Sudan da kuma ‘yan adawar ‘Rapid Support Forces’ (RSF), sun amince da tsagaita wuta na kwanaki bakwai.

Blinken ya ce yayin da irin wannan yarjejeniyoyin suka kasa cika a baya, a wannan karon ɓangarorin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta kwashe dukkan ‘yan kasarta da suka maƙale a birnin Khartoum na Sudan

Bugu da ƙari, za a kafa wata hanyar sanya ido da Amurka da Saudiyya ke tallafawa don bayar da rahoton karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Ɓangarorin biyu sun bayyana aniyarsu ta yin aiki da yarjejeniyar. An daɗe ana gwabzawa a kan madafun iko a ƙasar a yankin kahon Afirka a ranar 15 ga Afrilu.

Dakarun da ke ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Abdel Fattah al-Burhan na fafatawa da dakarun sa-kai na mataimakinsa Mohammed Hamdan Daglo. Janar-janar biyu sun ƙwace mulki tare a shekara ta 2021, amma daga baya suka faɗi.

2 COMMENTS

Leave a Reply