Ana matsa min lamba na koma jam’iyyar APC – Gwamnan Mufwang 

0
126
Ana matsa min lamba na koma jam'iyyar APC - Gwamnan Mufwang 
Gwamna Mufwang na Filato

Ana matsa min lamba na koma jam’iyyar APC – Gwamnan Mufwang

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa yana shan matsin lamba daga wasu jiga-jigan siyasa don ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC.

Ya bayyana hakan ne a wani taron da aka gudanar a gidan gwamnati, Jos, inda ya ce Allah da jama’ar da suka zaɓe shi ne kaɗai za su iya yanke masa hukuncin sauya jam’iyya.

“Sun matsa min lamba, amma na gaya musu cewa sai Allah da ku jama’a ne za su bani izini,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Filato ta kama ‘yar fafutuka saboda fallasa gazawar gwamnati – ‘Yan Najeriya na sukar matakin

Ya tambayi jama’a ko sun umarce shi da sauya jam’iyya, inda suka amsa da ƙarfi da cewa “A’a.”

Wannan furuci na Mutfwang ya biyo bayan rahotannin da suka ce APC a Filato na ƙoƙarin jawo shi zuwa jam’iyyarsu, lamarin da jiga-jigan APC suka yi watsi da shi.

Gwamnan ya ce waɗanda ke adawa da jita-jitar sauya shekar tasa suna yin hakan ne saboda tsoro, yana mai cewa da yawancin ‘yan APC a Filato za su yi farin cikin ganin ya shiga jam’iyyarsu.

Tun bayan zaɓen 2023, PDP ta rasa gwamnoni uku zuwa APC, yayin da wasu gwamnoni a Taraba, Zamfara da Osun ke zargin suna shirin komawa jam’iyyar mai mulki.

Leave a Reply