No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ana ci gaba da gwabza faɗa a gabas ta tsakiya

An gwabza faɗa a ɓangarori da dama a Yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Alhamis, inda aka kashe aƙalla mutum 16.

Hukumomi sun ce makamai masu linzami da aka harbo daga Lebanon sun kashe mutum biyar a arewacin Isra’ila, ciki har da wani manomi da wasu ma’aikata ‘yan kasashen wajen hudu.

Lebanon ta ce hare-haren Isira’ila sun kashe akalla mutum takwas, ciki har da ma’aikatan lafiya shida a kudancin kasar.

KU KUMA KARANTA:Mun kammala kai hare-haren da muka tsara kaiwa Iran – Isra’ila

A halin da ake ciki, jami’an Falasdinawa sun ce wani harin Isra’ila a Yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye ya kashe mutum uku.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kuma kai hari kan wuraren ajiyar makamai da sansanoni a Syria, inda ta yi ikirarin cewa kungiyar mayakan a baya-bayan nan ta fara ajiye makamai a kan iyakar Syria da Lebanon, domin yin fasakaurin su zuwa Lebanon.

Isra’ila ta ba da sanarwar ficewa ta gargadin ga mazauna Baalbek a gabashin Lebanon a rana ta biyu a jere.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...