An zaɓi Farfesa Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa 

0
318
An zaɓi Farfesa Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa 
Sabon shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda

An zaɓi Farfesa Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa

Jam’iyyar APC ta zaɓi Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar na ƙasa. Zaɓen ya gudana ne a ranar Alhamis yayin zaman Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar, inda aka zaɓe shi ba tare da hamayya ba, don maye gurbin Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya sauka daga mukamin bisa wasu dalilai na lafiya.

Farfesa Nentawe, wanda aka haifa a ranar 8 ga watan Agusta, 1968 a garin Dungung, ƙaramar hukumar Kanke ta Jihar Filato, fitaccen masani ne a fannin Injiniyan na’ura mai kwakwalwa da Lantarki. Ya yi karatunsa na farko a Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Makurdi, sannan ya samu digirinsa na biyu daga ATBU Bauchi, da kuma digirin digirgir daga Jami’ar Najeriya Nsukka. Ya kwashe sama da shekaru 26 yana koyarwa da gudanar da manyan ayyuka a jami’o’i, kuma ya taka rawa a matsayin darektan ICT na farko a jami’ar Makurdi.

KU KUMA KARANTA: Ganduje ya Ajiye mukaminsa na Shugabancin Jam’iyar APC na Ƙasa

Baya ga aikin ilimi, Farfesa Yilwatda ya taka rawa a bangaren kirkire-kirkire da sauyi ta fannin fasaha a ciki da wajen gwamnati. A matsayinsa na kwararre a harkar sadarwa da fasahar zamani, ya yi aiki da manyan kungiyoyin duniya irinsu EU, UNICEF, Bankin Duniya da TECHVILE USA. A shekarar 2017, ya zama kwamishinan zaɓe na INEC, inda ya kawo muhimman sauye-sauye a tsarin zaɓe da suka haɗa da tsarin kada kuri’a ga ’yan gudun hijira da masu buƙata ta musamman.

Yanzu da ya zama shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Yilwatda ya shigo da ƙwarewa ta musamman, hangen nesa, da sadaukarwa da zai amfani jam’iyyar da ƙasa baki ɗaya. A matsayinsa na shugaban kamfen ɗin Tinubu/Shettima a Jihar Filato, kuma Ministan Jinƙai, yana da zurfin alaƙa da ɓangarori da dama na gwamnati da ƙungiyoyin ci gaba, wanda hakan zai taimaka wajen jagorantar jam’iyya cikin hadin kai da nasara.

Leave a Reply